Abubuwa 7 da Tinubu Ya Iske a Ofis da Suka Hana Shi Zuwa Taron Majalisar Dinkin Duniya
Abuja - A makon nan Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya dawo Najeriya bayan ya shafe kwanaki masu yawa a kasashen ketare.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci kasar Sin, Hadaddiyar daular Larabawa da Birtaniya kafin ya dawo a makon nan.
Bola Tinubu ba zai je taron MDD ba
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yarda cewa akwai ayyuka da yawa a gabansa, saboda haka ne ya fasa komawa taro a Amurka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kashim Shettima ne zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron majalisar dinkin duniya yayin da Tinubu ke fama da rikicin gida.
Rahoton nan ya tattaro abubuwan da za su ba shugaba Tinubu ciwon-kai daga dawowarsa don haka za a bukaci shawo kansu.
1. Ambaliyar Maiduguri
Shigowarsa Najeriya yake da wuya sai aka ji Bola Tinubu ya isa jihar Borno domin jajantawa al’umma kan ambaliyar da aka yi kwanaki.
Shugaban kasar ya dauki wasu matakai dabam-dabam kuma ana sa ran gwamnatinsa ta magance aukuwar matsalar a sauran jihohi.
2. Karin kudin fetur
A duk fadin Najeriya yanzu ana kuka game da karin farashin man fetur da aka yi inda aka ji cewa lita ta doshi N1, 000 a wasu garuruwan.
An samu karin ne lokacin da aka fara tace mai a gida saboda haka dole shugaban kasa ya kawo karshen sabanin kamfanin Dangote da NNPCL.
3. ‘Yan bindiga a jihohin Arewa
Dama can mai girma shugaban kasa ya bukaci a ga bayan ‘yan bindigan da suka addabi musamman jihohin da ke Arewa maso yamma.
An yi nasarar hallaka Halilu Buzu da wasu miyagun, shugaban kasan yana sa rai sojoji su ga bayan irinsu Bello Turji da ake nema ido rufe.
4. Barazanar ‘yan kwadago
‘Yan kwadago da ‘yan fansho sun fara nuna cewa tun da kudin fetur ya tashi, ba za ta yiwu N70, 000 ya zama mafi karancin albashi ba.
Shugaban NLC, Kwamred Joe Ajaero ya nuna za a koma teburin zama da gwamnatin tarayya a sakamakon tashin farashin man fetur.
5. ASUU da ma’aikatan jami’o’i
Bayan kungiyoyin NLC da NUP, shugaba Tinubu zai yi fama da ma’aikatan jami’o’i; NASU da SSANU da ke barazanar yajin aiki a kasar.
Kafin tafiyarsa Sin, UAE da Birtaniya, gwamnatinsa ta na kokarin tattaunawa da shugabannin ASUU domin hana ta rufe jami’o’i.
6. Zaben gwamnan Edo
Yanzu kowa dai ya zura ido domin ganin yadda hukumar INEC za ta gudanar da zaben sabon gwamnan jihar Edo a karshen makon nan.
Jam’iyyar shugaban kasar watau APC ta dage sai ta karbe jihar daga hannun Godwin Obaseki da PDP da ke zargi jami’an tsaro da son-kai.
7. Canji a gwamnatin tarayya
Bayan dawowar shugaban kasa aka ji ya gana da Farfesa Attahiru Jega wanda ya gabatar da rahoton kafa ma'aikatar raya kiwon dabbobi.
Ana rade-radin za a yi sauyi a gwamnatin tarayya kuma watakila shugaban kasar ya rusa wasu ma'aikatu idan ya tashi sauya ministoci.
Sojoji sun kashe Halilu Buzu
‘Dan ta’ddan nan Halilu Sabubu Buzu wanda aka ce uban gidan Bello Turji ne ya tafi inda kowa zai je kamar yadda rahoto ya bayyana a baya.
A wani kauye dakarun Operation Hadarin Daji suka yi wa ‘yan bindigan kwantan bauna. Bayan bindige Buzu, ana neman Bello Turji yanzu.
Asali: Legit.ng