Ma'aikata Sun Caɓa, Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Watan da Za a Fara Biyan Albashin N70,000

Ma'aikata Sun Caɓa, Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Watan da Za a Fara Biyan Albashin N70,000

  • Gwamnatin Bola Tinubu ta fadi lokacin da fara biyan mafi ƙarancin albashin N70,000 zai soma aikin bayan an amince da ƙarin
  • Kwamitin tsarawa da gyara albashin ma'aikata (NSIWC) ya yi zama na musamman kan fara biyan mafi ƙarancin albashin
  • Yayin zaman a yau Juma'a 20 ga watan Satumbar 2024, kwamitin ya ce za a fara biyan albashin tun daga watan Yulin wannan shekara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta yi magana kan lokacin fara biyan mafi ƙarancin albashin N70,000.

Kwamitin gyara albashin ma'aikatan ya amince da tabbatar da fara biyan tun daga watan Yulin 2024.

Gwamnatin Tinubu ta fadi lokacin fara biyan albashin N70,000
Gwamnatin Tarayya za ta kaddamar da mafi ƙarancin albashi daga watan Yuli. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

An fadi watan fara biyan karin albashi

Kara karanta wannan

Kuɗin fetur: Yan kwadago sun raina sabon albashin N70,000, za su sake bugawa da Tinubu

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar bayan ganawa a Abuja a yau Juma'a 20 ga watan Satumbar 2024, cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamitin ya ce za a tabbatar da biyan albashin ne daga 29 ga watan Yulin 2024 watanni biyu kenan zuwa yanzu.

"Kwamitin NSIWC zai fitar da jadawalin tsare-tsaren albashi domin tabbatar da shi."
"Lokacin da za a tabbatar da fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin shi ne 29 ga watan Yulin 2024."

- Cewar sanarwar

Musabbabin kafa kwamitin sabon albashin N70,000

Tun farko an kafa kwamitin ne domin tabbatar da biyan mafi ƙarancin albashin N70,000 Najeriya.

Kwamitin ya ƙunshi akalla mambobi 16 domin tattaunawa da kuma amincewa da tabbatar da biyan mafi ƙarancin albashin, The Nation ta ruwaito.

Hakan ya biyo bayan amincewa da karin mafi ƙarancin albashi daga N30,000 zuwa N70,000 duba da halin kunci da al'umma ke ciki a kasar.

Kara karanta wannan

Gwamna ya bi sahun takwarorinsa a shirin fara biyan ma'aikata sabon albashin N70,000

Tinubu ya gargadi ma'aikatu kan albashin N70,000

Mun ba ku labarin cewa Gwamnatin Tarayya ta yi barazanar tasa keyar duk ma'aikatu zuwa gidan yari da suka gaza biyan mafi ƙarancin albashi.

Gwamnatin ta ce biyan mafi ƙarancin albashi N70,000 shi zai rage radadin da al'umma ke ciki na mawuyacin hali.

Wannan na zuwa ne bayan tabbatar da mafi ƙarancin albashin N70,000 a matsayin doka a fadin kasar baki daya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.