Bayan Kama Matashi da Sata a Kano, Masu Kaya Sun Fadi Sharadin Yafe Masa
- Jami'an bijilanti sun tarfa wani matashi dan asalin Katsina bayan zargin da ake yi masa na kutsa wa gidan mutane
- Ana zargin matashin mai shekaru 20 da satar kayan abinci, wayoyin hannu da karafa wanda tuni ya sayar da su
- Mutanen da ya shiga gidajensu sun bayyana cewa za a yafe masa, amma akwai babban sharadin da zai cika tukun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - An kama wani matashi, Mujahid Idris dan asalin jihar Katsina mai shekara 20 da ake zargi da shiga gidajen wasu mutane a jihar Kano ya na satar abinci.
Jami'an kungiyar tsaron sa kai da aka fi sani da bijilanti ne su ka yi ram da matashin bayan nemansa ruwa a jallo
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa ana zargin matashin da haura wa gidajen mutane a Mariri Gadon Arewa da ke karamar hukumar Kumbotso.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutanen da ya shiga gidajensu tare da yin satar sun amince da yafe masa, amma da sharadin ba zai sake zama a jihar Kano ba.
Ana zargin matashi da satar abinci
Jami'an sa kai ba kungiyar bijilanti sun bayyana kama matashin mai suna Mujahid Idris bayan an yi masa tara-tara bisa zargin satar kayan abinci.
Kwamandan bijilanti na karamar hukumar Kumbotso, Sani Abdullahi ya ce sun dade su na farautar matashin, amma sai yanzu aka yi nasarar kama shi.
Abubawan da ake zargin matashin ya sace
Kwamandan bijilanti ya lissafa wasu daga cikin kayan da ake zargin Mujahid da sace da suka hada da kayan abinci da kayan karafa da yace tuni ya sayar da su.
Sauran abubuwan da ya amsa cewa ya sata sun hada da wayoyin Android da kudade, wanda tuni ya batar da su.
Kishi: Ana zargin ba yaro guba a Kano
A wani labarin kun ji cewa an kama wata mata, tare da gurfanar da ita a gaban kotu kan zargin kashe karamin yaro mai shekara daya tal da haihuwa.
Barista Abdussalam Dan Maidaki Sale wanda ya gabatar wa kotu tuhumar ya kafa hujja da cewa laifin ya sabawa dokoki da kundin tsarin mulki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng