Hukumar EFCC Ta Fadi yadda Aka yi Gumurzu kan Yunkurin Kama Yahaya Bello
- Hukuma mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta yi karin haske kan yunkurin kama Yahaya Bello da aka yi
- EFCC ta zargi gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo da boye Yahaya Bello yayin da jami'anta suka yi yunkurin cafke shi a makon nan
- Ana zargin tsohon gwamnan jihar Kogi ne kan karkatar da makudan kudi har Naira biliyan 80.2 kuma ana nemansa yanzu ido rufe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Hukuma mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta magantu kan yunkurin kama Yahaya Bello.
EFCC ta bayyana cewa ta samu katsalandan daga gwamnan jihar Kogi na yanzu wajen ba Yahaya Bello kariya.
Jaridar Punch ta wallafa cewa kakakin hukumar EFCC, Dele Oyewale ne ya bayyana yadda abin ya faru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
EFCC: Yadda aka so cafke Yahaya Bello
A ranar Laraba aka ji karan harbe harbe a wani gida yayin da jami'an hukumar EFCC suka yi yunkurin kama Yahaya Bello.
Hakan ya biyo bayan ikirarin da tsohon gwamnan jihar Kogin ya yi ne kan cewa ya mika wuya ga gayyatar da EFCC ta yi masa.
Haka dai jami'an EFCC suka gama kai ruwa rana gidan da suke zargi Yahaya Bello na ciki ba tare da sun samu kama shi ba.
'Ododo ya taimaki Yahaya Bello' inji EFCC
Hukumar EFCC ta ce abin da ya hana ta cafke Yahaya Bello shi ne kariyar da ya samu daga gwamna Usman Ahmed Ododo.
Legit ta ruwato cewa EFCC ta ce Usman Ahmed Ododo yana amfani da rigar kariya da yake da ita wajen boye Yahaya Bello daga kamu.
Manema labarai sun yi yunkurin ji ta bakin jami'an yada labaran Yahaya Bello amma ba su ba da amsa ba har a lokacin hada rahoton.
PDP ta bukaci EFCC ta binciki gwamna
A wani rahoton, kun ji cewa yayin da ake surutu kan gyaran rijiyoyi a jihar Sokoto, jam'iyyar PDP ta bukaci binciken Gwamna Ahmed Aliyu.
Rahotanni sun nuna cewa jam'iyyar PDP ta yi Allah wadai da sake ware makudan kudi har N30bn domin katange hanyoyi a jihar Sokoto.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng