Jega: Tsohon Shugaban INEC Ya Gana da Tinubu, An Fara Tunanin Za a Nada Minista

Jega: Tsohon Shugaban INEC Ya Gana da Tinubu, An Fara Tunanin Za a Nada Minista

  • Shugaba Bola Tinubu ya gana da tsohon shugaban hukumar INEC, Farfesa Attahiru Jega a fadar shugaban kasa a ranar Alhamis
  • A cewar rahoton da aka samu, Farfesa Jega ya je Aso Villa ne domin mika rahoton kwamitinsa kan ma’aikatar kiwo ga shugaban kasar
  • A farkon shekarar nan ne Tinubu ya nada Jega a matsayin shugaban kwamitin shugaban kasa kan aiwatar da sauye-sauyen kiwo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya karbi bakuncin Farfesa Attahiru Jega, tsohon shugaban hukumar INEC a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Alhamis.

A cewar fadar shugaban kasar, Attahiru Jega ya ziyarci fadar ne domin mika rahoton kwamitinsa kan shirin kaddamar da ma’aikatar kiwon dabbobi ga shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fasa halartar taron Majalisar Dinkin Duniya, an fadi dalilin zama a gida

Shugaba Bola Tinubu ya gana da Farfesa Attahiru Jega a Villa
Tinubu ya karbi rahoton kwamitin shugaban kasa kan kiwon dabbobi daga Jega. Hoto: @FMINONigeria
Asali: Twitter

Bola Tinubu ya gana da Attahiru Jega

Bayo Onanuga, mai magana da yawun Shugaba Tinubu ya wallafa hotuna da bayanai kan ziyarar a shafinsa na Twitter a ranar 19 ga Satumbar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Onanuga ya ce:

"Ma'aikatar kiwon lafiya na kan hanya: Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karbi rahoton kwamitin shugaban kasa kan aiwatar da sauye-sauyen kiwon dabbobi.
"Ya karbi rahoton daga hannun shugaban kwamitin, Farfesa Attahiru Jega a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Alhamis 19 ga Satumbar 2024."

Abin da rahoton Jega ya kunsa

Jaridar Independent ta rahoto Farfesa Jega ya gabatar wa Tinubu rahoton mai shafi 152 da ke bayani dalla-dalla kan matakan kawo sauyi a fannin kiwo.

Wani bangare na rahoton ya ba da shawarar tsarin da zai kawo sauyi a harkar kiwo cikin shekaru 10 wanda 'yan Najeriya da gwamnati za su ci gajiyar nasarorinsa.

Kara karanta wannan

Wahalhalu sun tsananta a Najeriya, Abdulsalami ya ba Tinubu muhimmiyar shawara

Kundin rahoton mai shafi 152 ya kuma hada da shawarwari kan yadda za a iya magance matsalolin da suka fi jawo rikicin manoma da makiyaya cikin ruwan sanyi.

Rahoton ya kuma hada da ka’idojin aiki na ma’aikatar raya dabbobi ta tarayya, sabuwar ma’aikatar da gwamnatin Tinubu ta kirkiro kwanan nan.

Tinubu ya ba Jega mukami a UDUS

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Tinubu ya nada Attahiru Jega, tsohon shugaban hukumar INEC a matsayin shugaban majalisar gudanarwa na jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Farfesa Attahiru Jega na cikin mutane 555 da shugaban kasar ya naɗa shuagabancin kwamitocin gudanarwa a manyan makarantu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.