Karin Albashi: Gwamna Zai Fara Biyan N70,000 a Watan Satumba

Karin Albashi: Gwamna Zai Fara Biyan N70,000 a Watan Satumba

  • Gwamnatin Ebonyi ta sanar da cewa shirye shiryen fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi sun kusa kammaluwa a jihar
  • Kwamishinan yada labaran jihar Ebonyi, Jude Okpor ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a yau Alhamis
  • Jude Okpor ya ce gwamnan jihar yana shirye da ya fara biyan ma'aikata sabon albashi a watan Satumba idan komai ya kammala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ebonyi - Gwamnatin jihar Ebonyi ta fitar da sanarwa kan biyan mafi ƙarancin albashi na N70,000.

Gwamnatin ta bayyana cewa a yanzu haka ana kan shirye shirye domin tabbatar da komai ya kammala.

Gwamnan Ebonyi
Gwamnan Ebonyi zai yi karin albashi. Hoto: Hon. Francis Ogbonna Nwifiru
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa kwamishinan yada labaran jihar Ebonyi, Jude Okpor ne ya fitar da sanarwar.

Kara karanta wannan

Gwamna ya bi sahun takwarorinsa a shirin fara biyan ma'aikata sabon albashin N70,000

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shirye shiryen karin albashi a jihar Ebonyi

Kwamishinan yada labaran jihar Ebonyi ya ce ana kan shirye shirye domin cika umarnin gwamna Francis Ogbonna Nwifiru.

Jude Okpor ya ce gwamna Francis ya riga ya ba shugaban ma'aikatan jihar umarnin samo cikakken bayani kan yadda za a kara albashin ma'aikata.

Saboda haka ya ce hukumomin da aka daura wa alhakin samar da rahoton suna aiki ba dare ba rana domin kawo bayani kuma sun kusa gamawa.

Yaushe za a fara biyan albashin N70,000 a Ebonyi?

Kwamishinan yada labarai, Jude Okpor ya ce bisa dukkan alamu kwamitin za su kammala aikinsu a cikin watan Satumban da muke ciki.

Saboda haka Jude Okpor ya ce gwamna ba zai yi wata wata ba da fara biyan albashin N70,000 a watan Satumba da zarar komai ya kammala.

Kara karanta wannan

NNPCL ya fadi lokacin da matatar man gwamnati za ta fara aiki gadan gadan

A cewar kwamishinan, hakan na cikin kokarin gwamna Francis Ogbonna Nwifiru na kyautatawa ma'aikatan gwamnati a jihar Ebonyi.

N70,000: Abba zai yi karin albashi a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta bai wa ma’aikatan jihar tabbacin biyan sabon mafi karancin albashi.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta fara biyan ma'aikata mafi karancin albashi na N70,000 daga mako mai zuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng