Rabi'u Kwankwaso Ya Bi Sawun Manyan Arewa, Ya Tallafa wa Borno da N50m

Rabi'u Kwankwaso Ya Bi Sawun Manyan Arewa, Ya Tallafa wa Borno da N50m

  • Tsohon dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ziyarci Maiduguri domin taya gwamna Babagana Zulum alhini
  • Kwankwaso, wanda tsohon gwamnan Kano ne ya bayyana bakin cikinsa kan afakuwar ambaliya da ta shafi sama da mutum miliyan biyu
  • A ziyarar da ya kai, jagoran tafiyar Kwankwasiyya na kasa, kuma jagoran NNPP ya bayar da tallafin Miliyoyin Naira ga gwamnatin Borno

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno - Tsohon dan takarar shugaban kasar nan, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya kai ziyarar jaje da taya alhini jihar Borno da ta ke fama da ambaliya.

A ziyarar da ya kai fadar gwamnatin jihar Borno da ke Maiduguri, Sanata Kwankwaso ya taya jama'ar Borno takaicin iftila'in da ya gigita jama'a.

Kara karanta wannan

Borno: Manya na ci gaba da zuwa jaje Maiduguri, an ƙara bada tallafin N50m

Kwankwaso
Sanata Kwankwaso ya ba Borno tallafin ambaliya Hoto: @HonAbdullahiM12
Asali: Facebook

A sakon da Kwankwason Tuwita ya wallafa a shafinsa na X, tsohon gwamnan Kano Kwanwaso ya mika tallafin Miliyoyin Naira ga gwamna Babagana Umara Zulum.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

N50m: Kwankwaso ya ba Borno tallafin ambaliya

Tsohon Sanata da ya wakilci Kano ta Tsakiya, Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayar da tallafin ambaliya ga gwamnatin jihar Borno.

Jagoran tafiyar Kwankwasiyyar na kasa ya bayar da Naira Miliyan 50 domin a kara kudin abinci ga jama'ar da ke cikin radadin iftila'in abinci, kamar yadda Governor Tweeter ya wallafa a shafin X.

Ambaliya: Kwankwaso ya ziyarci Borno

Tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi takakkiya zuwa Borno kwanaki tara bayan mummunar ambaliya.

Mutane sama da 37 ne aka tabbatar sun rasu a ambaliyar da ta mamaye akasarin Maiduguri; babban birnin Borno.

Kara karanta wannan

Ambaliyar Maiduguri: 'Yan siyasa sun zabura, majalisar wakilai ta tallafa da N100m

Yan majalisa sun tallafawa Borno bayan ambaliya

A baya, mun kawo labarin yadda tawaga daga majalisar dattawan kasar nan ta ziyarci Maiduguri domin mika ta'aziyya bayan rasuwar wasu mazauna Borno sakamakon ambliya.

A ranar Talata ne ruwan da ke madatsar Alau ya hauro cikin gari, inda ya mamaye da yawa Maiduguri wanda ya jawo asarar miliyoyi, rayukan jama'a da dabbobi da rasa gonakin noma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.