Gwamna Ya Faɗi Tsohon Gwamnan da Yake Zargi da Alaƙa da Ƴan Bindiga

Gwamna Ya Faɗi Tsohon Gwamnan da Yake Zargi da Alaƙa da Ƴan Bindiga

  • Gwamna Dauda Lawal ya ce a bayanan da ya tattara, tsohon gwamna Bello Matawalle na da hannu a ayyukan ƴan bindiga a Zamfara
  • Dauda Lawal ya shawarci Matawalle ya yi murabus daga matsayin ƙaramin ministan tsaro domin ya fuskanci zarge-zargen da ake masa
  • Mai girma Gwamnan ya kuma zargi Matawalle da almubazzaranci da dukiyar jihar Zamfara tare da yin sakaci da sha'anin tsaron Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara - Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya zargi magabacinsa, Bello Matawalle da hannu dumu-dumu a ayyukan ‘yan bindiga da suka addabi jihar.

Dauda Lawal ya yi ikirarin cewa bisa ga bayanan da ya tattara, gwamnatin tsohon gwamnan ta riƙa ɗasawa da manya-manyan ƴan bindiga a Zamfara.

Kara karanta wannan

Dattawan Zamfara sun ba Gwamna Dauda shawara kan Matawalle

Gwamna Dauda Lawal da Matawalle.
Gwamna Dauda Lawal ya zargi Matawalle da hannu a ayyukan ƴan bindiga a Zamfara Hoto: Dauda Lawal, Muhammad Bello Matawalle
Asali: Twitter

Gwamnan ya yi wannan zargin ne yayin da yake jawabi a cikin wani shirin gidan talabijin na TVC da suka wallafa a dandalin Youtube ranar Laraba da daddare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dauda Lawal ya kuma zargi gwamnatin da ta gabata karkashin Matawalle, karamin ministan tsaro na yanzu, da yin kashe mu raba da dukiyar al'ummar Zamfara.

Gwamna Lawal ya gano bayanai kan Matawalle

A cewarsa, gwamnatin Matawalle ta yi sakaci da sassauci a batun magance matsalar ƴan bindiga, wanda jihar ta shafe shekaru ta na fama da su.

"E, gaskiya akwai batutuwa da yawa da suka shafi magabacina. Bari ku ji a takaice da ni ne shi (Matawalle) zan yi murabus na fuskanci duk wani zargi da ake mani."
"Daga dukkan bayanan da muke samu, wanda na gada (Matawalle) na da hannu dumu-dumu a wasu daga cikin harkokin ‘yan fashin daji,” in ji Lawal.

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda ya fadi lokacin gamawa da Turji, ya tona abin da ke rura wutar

Dalilin gwamnan Zamfara na zargin Matawalle

Da yake kafa hujjojin da ya sa yake zargin Matawalle, gwamnan ya bayyana yadda babban sakatare a gwamnatin Matawalle ya biya kuɗin fansar ƴaƴansa ta gidan gwamnati.

A ruwayar Punch, Lawal ya ƙara da cewa:

"Bisa baganan da muka tono, ya bayyana ƙarara cewa ‘yan bindigar na samun mafaka a gidan gwamnati (lokacin mulkin Matawalle), sannan akwai wasu batutuwa da dama.”

Dauda Lawal ya kara da cewa, da shi ne Matawalle, da ya yi murabus nan take domin wanke kansa daga duk wani zargi.

Matawalle: Dattawa sun ba Gwamna Lawal shawara

A wani rahoton wata ƙungiyar dattawan Zamfara ta ba gwamnan jihar shawara kan abin da ya kamata yafi maida hankali a kansa a mulki.

Ƙungiyar ta buƙaci Gwamna Dauda Lawal da ya ba da fifiko wajen sauke nauyin da ke kansa maimakon sukar Bello Matawalle dare da rana.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262