Ambaliyar Maiduguri: Gwamnatocin Jihohi 9 da Suka ba Borno Tallafin Naira Biliyan 1.1

Ambaliyar Maiduguri: Gwamnatocin Jihohi 9 da Suka ba Borno Tallafin Naira Biliyan 1.1

  • Gwamnatocin jihohi 9 wadanda dukkaninsu na Arewacin kasar nan ne sun ba da gudunmawar Naira biliyan 1.1 ga jihar Borno
  • Wannan tallafin na zuwa ne yayin da ambaliyar ruwa ta mamaye sassan Maiduguri, babban birnin Borno a makon jiya
  • Legit Hausa ta tattaro jerin gwamnatocin jihohin da suka kai wa Borno dauki da kuma adadin kudin da kowacce jihar ta bayar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - A ranar Litinin, 9 ga Satumbar 2024 'yan Maiduguri da ke jihar Borno suka wayi gari da ambaliyar ruwa da ta mamaye kusan gaba daya garin.

Gwamnatocin Najeriya, musamman na Arewa da ma gwamnatin tarayya sun ba da tallafi daban daban tare da jajantawa wadanda ambaliyar ta shafa.

Kara karanta wannan

Bayan tallafin biliyoyi, gwamnatin Borno ta fitar da gudunmawar ambaliya da ta samu

Jihar Borno ta samu tallafin N1.1bn daga gwamnatocin jihohi 9 na Arewa
Bayan ambaliyar Maiduguri, gwamnatocin jihohi 9 na Arewa sun ba Borno tallafin N1.1bn. Hoto: @Miqdad_Jnr, @SenBalaMohammed, @NasiridrisKG
Asali: Twitter

Ga jerin gwamnatocin jihohi takwas da suka ba jihar Borno tallafin miliyoyin Naira da adadin kudin da kowanne gwamna ya bayar kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Gwamnatin Bauchi: N250m

Gwamnatin jihar Bauchi ta bayar da gudunmawar Naira miliyan 250 ga wadanda ambaliyar ruwa ta rutsa da su a jihar Borno domin rage radadin da suke fuskanta.

2. Gwamnatin Kebbi: N200m

Har ila yau rahotanni sun ce gwamnatin Kebbi ta ba da Naira miliyan 200 domin tallafawa wadanda masifar ambaliyar ruwan ta auka masu.

3. Gwamnatin Yobe: N100m

Gwamna Mai Mala Buni wanda yake rike da gwamnatin Yobe ya ba makwabtansa (Borno) Naira miliyan 100 a sakamakon barnar da aka samu.

3. Gwamnatin Yobe: N100m

Ita ma gwamnatin Taraba ta aiko da gudumuwar ambaliyar ruwan. Gwamnatin Borno ta samu Naira miliyan 100m daga jihar.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Yan majalisar dattawa sun ziyarci Borno, sun mika tallafin N74m

5. Gwamnatin Katsina: N100m

Sannan ana da labari Gwamna Dikko Radda da wasu manya sun ziyarci Borno a makon nan, gwamnatin Katsina ta ba da tallafin Naira miliyan 100.

6. Gwamnatin Gombe: N100m

Gwamnan Gombe, Muhammadu Yahaya, wanda ya samu wakilcin wata babbar tawaga, ya ba da tallafin Naira miliyan 100 ga jihar Borno.

7. Gwamnatin Kano: N100m

Mun rahoto cewa wata tawagar gwamnatin Kano ta dura Borno, inda ta yi jajen ambaliyar Maiduguri tare da ba jihar tallafin Naira miliyan 100 a madadin Abba Kabir Yusuf.

8. Gwamnatin Kaduna: N100m

Mataimakiyar gwamnan Kaduna, Dakta Hadiza Balarabe ta jagoranci tawaga zuwa jihar Borno, inda ta mikawa Zulum Naira miliyan 100 domin tallafawa wadanda ambaliya ta shafa.

9. Gwamnatin Adamawa: N50m

Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ya ba gwamnatin Borno tallafin Naira miliyan 50 da kuma jiragen ruwa shida domin ayyukan jin kai bayan ambaliyar Maiduguri.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Dattijon attajiri, Dantata ya tallafa wa Borno da sama da Naira biliyan 1

"Mukaddari ce": Tinubu ga 'yan Borno

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce babu wani mutum da ya haddasa ambaliyar ruwa a Maiduguri, don haka ka da a zargi kowa.

Shugaban kasar ya nemi 'yan jihar Borno da ma kasar baki daya da su dauki ambaliyar Maiduguri a matsayin mukaddari daga Allah SWT wanda babu wanda zai iya hanawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.