Sojoji Sun Cafke Masu Garkuwa da Mutane a Taraba, Sun Kwato Makamai

Sojoji Sun Cafke Masu Garkuwa da Mutane a Taraba, Sun Kwato Makamai

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar cafke wasu mutane da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a jihar Taraba
  • Sojojin na rundunar 'Operation Whirl Stroke' sun cafke waɗanda ake zargin ne bayan sun samu bayanan sirri kan ayyukansu
  • Ana dai zargin mutanen da suka haɗa da laifukan yin fashi da makami, garkuwa da mutane da sayar da makamai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Taraba - Dakarun sojoji na 'Operation Whirl Stroke' sun cafke wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a ƙaramar hukumar Karim Lamido ta jihar Taraba.

Sojojin sun cafke mutanen ne tare ƙwato bindiga ƙirar AK-47 da alburusai a wani samame da suka kai a ranar, 16 ga watan Satumban 2024.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan bindiga, sun ceto mutum 20 da aka sace

Sojoji sun cafke masu garkuwa da mutane a Taraba
Sojoji sun kama wadanda ake zargi da yin garkuwa da mutane a Taraba Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Sojoji sun cafke miyagu a Taraba

Tashar Channels tv ta rahoto cewa muƙaddaashin mataimakin daraktan yaɗa labarai na rundunar, Kyaftin Olubodunde Oni, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olubodunde Oni ya bayyana cewa dakarun sun samu bayanan sirri ne kan ayyukan rashin gaskiya da mutanen ke yi, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Mutanen dai an daɗe ana nemansu kan zargin aikata laifuffuka da suka haɗa da fashi da makami, garkuwa da mutane da sayar da makamai.

Yadda aka cafke waɗanda ake zargin

Sanarwar ta bayyana cewa an cafke ɗaya daga cikinsu mai suna Ali Tambaya a ƙauyen Wanzani ɗauke da bindiga ƙirar AK-47 da alburusai 42 masu ƙaurin 7.62mm.

A yayin da ake bincike ya amsa cewa ya siyo bindigar ne daga wajen wani Alhaji Dandi kan kuɗi N500,000 kusan shekara biyar da suka wuce sannan ya siyo alburusan kan kuɗi N1000 kowannensu.

Kara karanta wannan

NMA ta hango wata matsala bayan ambaliya a Maiduguri, ta ba da mafita

Ya kuma bayyana cewa wani mutum mai suna Alhaji Kiwo ne ya ba shi alburusai 38 daga cikin guda 42 ɗin domin ya ajiye masa.

Daga nan sai dakarun sojojin suka bi sauran waɗanda ake zargin inda suka cafke Alhaji Dandi yayin da suke ci gaba da ƙoƙarin cafke Alhaji Kiwo.

Sojoji sun hallaka ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu nasarar kashe ƴan bindiga mutum huɗu yayin wani artabu a jihar Kaduna.

Sojojin sun kuma samu nasarar kuɓutar da wasu mutane 20 da aka yi garkuwa da su a wani samame da suka kai a ƙananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa a jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng