Matasa Sun Shuna wa Yan Sanda Manyan Karnuka, Magana Ta Shiga Kotu

Matasa Sun Shuna wa Yan Sanda Manyan Karnuka, Magana Ta Shiga Kotu

  • Wasu matasa sun gamu da fushin hukuma bayan an gurfanar da su gabanta kan zargin cin zarafin jami'an yan sanda
  • Yan sanda na kokarin kama wani da ake zargi da aikata laifi sai mutanen biyu su ka kori jami'an tsaron da karnuka
  • Kotun da k Oyo ta aika mutanen kurkuku kafin sake ci gaba da zama a rana ta gaba inda za a ji yadda aka haihu a ragaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar OyoKotun majistare da ke zamanta a Ibadan ta aika da wata mata, Olayinka Akinware da wani Tunji Adesina bisa cin zarafin yan sanda.

Kara karanta wannan

Kwanaki 3 kafin zabe, gwamnan Edo ya raba kyautar Naira biliyan 1 ga mata

Ana zargin mutanen biyu da zargin shuna wa yan sanda karnuka hudu domin hana su kama wanda ake zargi da aikata laifi.

Police
Wasu matasa sun fuskanci fushin kotu Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard wallafa cewa ana zargin mutanen biyun da hada kai wajen hana doka yin aikilokacin da ya dace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An maka matasa kurkuku kan yan sanda

Daily Post ta wallafa cewa Mai Shari’a M. Mudashiru ya ki amince wa da rokon wadanda ake zargi, inda aka mika su kurkurkun Abolongo da ke jihar Oyo.

Mai Shari’ar ya bayyana cewa za a ci gaba da tsare wadanda ake zargi har sai an samu shawara daga ofishin da ke shigar da kara.

Cin zarafin yan sanda: An dage sauraron shari’a

Tun da fari, mai shigar da kara, Sufeto Femi Oluwadare ya shaida wa kotu cewa mutanen biyu sun take doka wajen hana bincike.

Alkali M. Mudashiru ya dage ci gaba da zaman shari’ar zuwa 18 Disamba, 2024 kan zargin cin zarafin jami’an tsaro.

Kara karanta wannan

Sojoji sun bude wuta, an damke masu taimakon 'yan bindigan Arewa da makamai

Yan sanda za su dakile ta'adanci

A baya kun ji cewa rundunar yan sandan kasar nan ta fara daukar wasu matakai da za su taimaka mata wajen fatattakar yan ta'addan da su ka addabi 'yan Najeriya.

Sufeton yan sanda na kasa, IGP Kayode Egbetokun ne ya bayyana haka inda ya ce an yi garan bawul ga manyan jami'an tsaro a wasu jihohin kasar nan a salon sake dabarun tabbatar da tsaro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.