'Hamster' na Shirin Fashewa, An Haramtawa Ma'aikatan Asibitin Tarayya 'Kirifto'
- Yayin da harkokin 'kirifto' da 'mining' suka zama ruwan dare, hukumomi sun fara daukar matakai kan lamarin a Najeriya
- Asibitin Gwamnatin Tarayya (FTH) da ke Gombe ya haramtawa ma'aikata 'kirifto' da 'mining' yayin da suke bakin aiki
- Hukumomin suka ce sun dauki matakin ne domin kare faruwar salwantar da rayuwa saboda yadda lamarin ke dauke hankali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Gombe - Hukumomi a Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Gombe sun sanya doka game da 'kirifto'.
Hukumomin sun haramtawa ma'aikata yin 'kirifto' ko 'mining' lokacin da suke bakin aiki.
An haramta 'mining' ga ma'aikatan asibiti
Mataimakin daraktan gudanarwa na asibitin FTH, Adamu Usman Tela shi ya bayyana haka ga jaridar Aminiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tela ya ce hukumomin asibitin sun lura cewa harkar 'mining' na dauke hankulan ma'aikata yayin da suke aiki.
Ya ce hakan yana da tasiri wurin rashin ba marasa lafiya kulawa ta musamman yayin da suke aiki.
Sanarwar ta ce an dauki matakin ne tun kafin fara samun matsalolin salwantar da rayuka saboda matsalar.
"Mun dauki mataki ne domin kare faruwar salwantar rayuwa, domin kula da lafiyar al’umma shi ne mafi muhimmanci.”
- Adamu Usman Tela
Yadda 'mining' ya yi tasiri ga matasa
Wannan na zuwa ne bayan matasa maza da mata sun rungumi harkar 'mining' domin samun na kashewa.
Wasu na ganin 'mining' na dauke hankulan mutane da dama musamman a wuraren aikinsu.
Sai dai matasa da dama suna yaba tsarin dangwale da ake yi da suka ce yafi wasu yan siyasar da dama da ke yaudarar al'umma.
Tattaunawar Legit Hausa da ma'aikacin FTH
Legit Hausa ta tattauna da wani ma'aikacin asibitin Tarayya da ke Gombe kan matakin haramta 'mining'.
Aliyu Dauda ya ce tabbas wannan mataki ne mai kyau wanda zai inganta aikin kula da marasa lafiya.
"Wannan lamari na 'mining' ko 'kirifto' abu ne da ke dauke hankali kan abin da zaka yi wa kanka bare kuma abin da yafi wani."
"Gaskiya daukar wannan mataki a dai dai wannan lokaci abin a yaba ne, hakan ya nuna hukumomin asibitin sun yi tunani sosai."
"Saboda rashin wadata na albashi ya sanya ma'aikata shiga wannan harka amma matakin ya kamata saboda kula da marasa lafiya abu ne mai muhimmanci."
- Aliyu Dauda
Ya ce duk da zamani ne hakan amma idan bai zama dole ba ya kamata ko waya bai kamata kana tabawa ba a asibiti saboda buƙatar kulawa da marasa lafiya.
Malamai sun fadi Halaccin 'mining' a Musulunci
Mun ba ku labarin cewa bayan fashewar notcoin (NOT), 'yan Najeriya maza da mata, babba da yaro sun raja'a a kan harkar
Wannan ya jawo tambayoyi suka yawaita kan matsayin mining a addinin musulunci saboda mutane na tsoron cin kudin haram.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng