Shirin Tsige Sanusi II a Sarautar Kano: Ganduje Ya Fadi Rawar da Ya 'Taka'

Shirin Tsige Sanusi II a Sarautar Kano: Ganduje Ya Fadi Rawar da Ya 'Taka'

  • Shugaban jam'iyyar APC mai mulki ya yi martani kan rahotannin da ke cewa yana da hannu a shirin tsige Muhammadu Sanusi II daga sarautar Kano
  • Abdullahi Umar Ganduje ya musanta raɗe-raɗin waɗanda ya bayyana a matsayin ƙarya da ƙarairayi
  • Ganduje ya bayyana cewa a yanzu babu ruwansa da abin da ya shafi sarautar Kano domin ba shi ba ne gwamnan jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi martani kan raɗe-raɗin da ke cewa yana da hannu a shirin tsige Muhammadu Sanusi II daga kan sarautar Kano.

Ganduje ya ƙaryata raɗe-raɗin inda ya bayyana su a matsayin tsantsagwaron ƙarya.

Ganduje ya magantu kan shirin tsige Sanusi II
Ganduje ya nesanta kansa da shirin tsige Sanusi II Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje, Masarautar Kano
Asali: Facebook

Ganduje ya musanta zargin da ake yi masa

Kara karanta wannan

Sarki mai martaba a Arewa ya kare Shugaba Tinubu, ya faɗi namijin ƙokarin da yake yi

Jaridar Leadership ta ce Ganduje ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Cif Oliver Okpala, ya fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban na APC yana mayar da martani ne kan wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda ya yi iƙirarin cewa Ganduje yana jagorantar tsige Muhammadu Sanusi II daga kan sarautar Kano.

Me Ganduje ya ce kan tsige Sanusi II

Da yake mayar da martani, Ganduje ya ce babu ƙamshin gaskiya a cikin iƙirarin, inda ya nanata cewa ba shi da hannu a zargin da ake yi na shirin tsige Sanusi II.

"Yana da kyau a sani cewa Ganduje ba shi da wata alaƙa ta naɗawa ko tsige Sarki Muhammadu Sanusi II a Kano."
"Ya kamata a sani cewa Ganduje yanzu ba shi ba ne gwamnan Kano ko shugaban majalisar dokokin jihar Kano, saboda haka ba shi da wata alaƙa da sarautar Kano."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai farmaki, sun yi garkuwa da wani shugaban al'umma

- Cif Oliver Okpala

A cewar sanarwar, Ganduje ya ce ba shi da hannu a wajen ba da ga shawara ga Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya haƙura da sarautar Kano.

Karanta wasu labaran kan Sanusi II

Sanusi II ya je ta'aziyyar Dada Yar'adua

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya kai ziyara jihar Katsina domin gaisuwar rasuwar Hajiya Dada.

Mai martaba Sarkin ya nuna damuwa kan rashin dattijuwar da ita ce mahaifiyar tsohon shugaban kasa, Malam Umaru Musa Yar'Adua.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng