Ana Kukan Yunwa, an Dawo da Harajin Tsaron Yanar Gizo a Sabon Tsari
- Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kara fitar da sabuwar sanarwa kan karɓar harajin tsaron yanar gizo daga yan Najeriya
- A wannan karon, Bankin CBN ya kawo canji a kan haraji da za a rika karba a hada hadar kudi da al'umma suka yi ta bankuna
- A watan Mayu ne gwamnatin tarayya ta soke harajin bayan yan Najeriya sun nuna kin amincewa da kirkiro karɓar shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sake bayani kan karɓar harajin tsaron yanar gizo wajen yan kasa.
A wannan karon, Bankin CBN ya sanar da rage kudin harajin a kan abin da ya yi niyyar karba a baya.
Jaridar Punch ta wallafa cewa a ranar Laraba ne Bankin CBN ya sake fitar da sanarwar kan karɓar harajin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Soke harajin tsaron yanar gizo a Najeriya
A watan Mayun da ya wuce Bankin CBN ya fito da tsarin karbar 0.5% a matsayin harajin tsaron yanar gizo.
Sai dai yan Najeriya, yan kwadago da wasu bankuna sun soki tsarin wanda hakan ya sa aka dakatar da shi.
Sabon harajin tsaron yanar gizo
Watanni uku bayan dakatar da tsarin, Arise News ta wallafa cewa babban Bankin CBN ya kara dawo da harajin a ranar Laraba.
Sai dai bayanai sun nuna cewa a wannan karon Bankin CBN zai rika karbar 0.005% ne maimakon 0.5% da ya yi niyya a karon farko.
Tsarin karbar harajin tsaron yanar gizo
Za a rika karbar harajin ne yayin da abokan hulɗar bankuna suka yi mu'amalar kudi ta kafar yanar gizo.
Sai dai an ce za a cire kudin karbar albashi, biyan bashi ko karbar bashi, tura kudi daga banki zuwa banki iri daya da sauransu daga cikin tsarin harajin.
Ana sa ran cewa za a rika amfani da kudin harajin ne a ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro domin yakar ta'addanci ta kafar yanar gizo.
CBN ya yi magana kan tallafin mai
A wani rahoton, kun ji cewa babban Bankin Najeriya CBN ya fitar da rahoto a kan matsalar da za a iya fuskanta kan cire tallafin fetur da gwamnati ta yi.
Bankin CBN ya kuma yi hasashen cewa za a fuskanci barazanar tattalin arziki kan yadda Najeriya ke kashe kudi a kan biyan bashi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng