Tambuwal: PDP Ta Yi Martani da Aka Tabo Binciken Tsohon Gwamna kan Satar N16bn

Tambuwal: PDP Ta Yi Martani da Aka Tabo Binciken Tsohon Gwamna kan Satar N16bn

  • PDP mai adawa ta yi martani bayan gwamnatin jihar ta fara binciken zargin karkatar da N16.1bn da ake yi wa Aminu Waziri Tambuwal
  • Jam'iyyar ta bayyana cewa jami'an gwamnatin tsohon gwamnan jihar a shirye suke su kai kansu gaban kwamitin binciken domin kare kansu
  • Gwamnatin jihar dai ta fara binciken Rt. Hon. Tambuwal ne bisa zargin karkatar da N16.1bn na hannun jarin Sokoto a lokacin mulkinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Jam’iyyar PDP reshen jihar Sokoto ta mayar da martani kan zargin karkatar da kuɗaɗen jihar da ake yiwa Aminu Waziri Tambuwal.

Ana zargin tsohon gwamnan da karkatar da hannun jarin Naira biliyan 16.1 na gwamnatin jihar.

Kara karanta wannan

Ayyukan ban mamaki 3 da Ahmad Aliyu ya kinkimo da ya zama Gwamnan Sokoto

PDP ta yi martani kan binciken Tambuwal
Ana zargin Aminu Tambuwal da karkatar da N16bn na Sokoto Hoto: @AWTambuwal
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaranta, Hassan Sahabi, jam'iyyar ta ce a shirye take ta kare kanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me PDP ta ce kan binciken Tambuwal?

Ta bayyana cewa dukkanin jami'an tsohuwar gwamnatin a shirye suke su kai kansu ga kwamitin binciken, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

"Dukkanin jami'an tsohuwar gwamnati a shirye suke su kai kansu ga kwamitin domin fayyace gaskiya kan batun karkatar da hannun jarin jihar da aka ƙirƙiro domin kawar da hankalin jama'a."
"Aminu Waziri Tambuwal ya gudanar da gwamnati mafi gaskiya da amana a tarihin jihar Sokoto, wanda hukumomi da dama na duniya sun tabbatar da hakan. Babu wani jami'in gwamnatin da zai ƙi amsa kiran doka."
"Sai dai, ba a samu irin hakan ba a wannan gwamnatin mai ci ta Ahmed Aliyu da ke cike da tarihin dambarwa wajen gudanar da harkokinta."

Kara karanta wannan

Gwamna a Arewa zai sauya sheka daga PDP zuwa APC? an ji gaskiyar lamari

- Hassan Sahabi

A tsaya a yi gaskiya

Dalhat Usman ya gayawa Legit Hausa cewa yana da kyau a tsaya a yi binciken bisa gaskiya domin gano haƙiƙanin yadda kuɗaɗen suka yi.

"Ba na tunanin cewa akwai siyasa a cikin binciken da za a yi. Fata na dai shi ne a tsaya a yi gaskiya a binciken. N16bn kuɗaɗe masu yawa waɗanda bai kamata a bari su tafi haka nan ba."

- Dalhat Usman

Jam'iyyar PDP ta buƙaci a bincike gwamna

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Sokoto ta bukaci a binciki ayyukan gwamnatin Gwamna Ahmed Aliyu na jihar.

Jam'iyyar PDP ta ce ya kamata hukumar yaƙi ds cin hanci da yiwa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta binciki ayyukan N30bn da gwamnan ya ware domin katangar hanya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng