Kano: An Sake Cafke Dan Jarida da Zargin Cin Mutuncin Abba Kabir, Sanusi II

Kano: An Sake Cafke Dan Jarida da Zargin Cin Mutuncin Abba Kabir, Sanusi II

  • Kotu ta sake cafke matashin dan jarida mai suna Muktar Dahiru tare da tasa keyarsa zuwa gidan yarin Kurmawa a Kano
  • Ana zargin Muktar da yada wasu abubuwa a kafofin sadarwa da suka ci zarafin Gwamna Abba Kabir da Sarkin Kano
  • Hakan ya biyo bayan ba da belinsa da aka yi amma bai cika ka'idojin ba kamar yadda lauyansa, Yusuf Isa ya fada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Kotun majistare a jihar Kano ta sake tura matashin dan jarida gidan gyaran hali na Kurmawa.

Ana zargin Muktar Dahiru da bata sunan Gwamna Abba Kabir da kuma Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Kotu ta mayar da matashi gidan kaso kan zargin cin mutuncin Abba Kabir
Kotu ya sake cafke dan jarida da zargin batanci ga Abba Kabir, Sanusi II. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Kano: An tura dan jarida gidan kaso

Kara karanta wannan

Sanata Abbo ya fadi abin da zai yi kan zargin lalata da matar aure, ya ba ta wa'adi

Premium Times ta ruwaito cewa kotun ta dauki matakin ne a zamanta a yau Laraba 18 ga watan Satumbar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin Muktar Dahiru da ke aiki da Pyramid FM kan yada wasu bayanai da ke nuna batanci ga Gwamna Abba Kabir da Muhammadu Sanusi II.

Lauyan Dahiru ya fadawa yan jaridu cewa an sake cafke matashin ne kwanaki biyu bayan an ba da belinsa.

Lauyan mai suna Yusuf Isa ya ce cafke shi ke da wuya aka sake tasa keyarsa zuwa gidan yarin Kurmawa

Ya ce kotun ta ce ta sake kama Dahiru ne saboda rashin cika ka'idojin ba shi beli da aka yi.

Zargin da ake yi wa dan jaridan

Wannan na zuwa ne bayan zargin dan jaridar da yada wata murya a hira da wani dan adawa kan zargin Abba Kabir da cin hanci da rashawa.

Kara karanta wannan

"Zai iya shiga kotu": Rundunar tsaro ta yi gargadi kan dambarwar Seamnan Abbas Haruna

A cikin hirar an jiyo dan siyasar na kalubalantar Abba Kabir da ya bari EFCC ta yi bincike kan badakalar Novomed madadin hukumar yaki da cin hanci a jihar.

Har ila yau, Dahiru ya yada wata murya da wani ke zargin Sanusi II da nuna kansa a matsayin mai tausayi alhali ba haka ba ne.

An kama hadimin Tambuwal a Sokoto

Kun ji cewa rundunar yan sanda a jihar Sokoto ta gurfanar da hadimin Sanata Aminu Tambuwal kan cin zarafin gwamna.

Ana zargin Shafi'u Tureta da cin mutuncin Gwamna Ahmed Aliyu inda ya wallafa faifan bidiyo da cewa bai iya yaren Turanci ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.