Ambaliya: Gwamna Radda Ya yi Ruwan Miliyoyi ga Talakawan Maiduguri

Ambaliya: Gwamna Radda Ya yi Ruwan Miliyoyi ga Talakawan Maiduguri

  • Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya hada tawaga mai karfi zuwa jihar Borno domin jajanta musu a kan ambaliyar ruwa
  • An ruwaito cewa tawagar ta hada da mai martaba Sarki Daura, kakakin majalisar jihar da wasu jami'an gwamnatin Katsina
  • Yayin mika sakon jaje, Gwamna Dikko Radda ya ba jihar da al'ummar da suka shiga ambaliyar gudunmawar N100m domin rage radadi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Gwamnatin jihar Katsina ta hada babbar tawaga zuwa Maiduguri domin yin jaje bayan ambaliyar ruwa.

Gwamna Dikko Umaru Radda ne ya jagoranci tawagar inda ya mika kyautar miliyoyi a matsayin tallafi domin rage radadi.

Gwamna Radda
Gwamna Radda ya ba Borno tallafin N100m. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Asali: Facebook

Legit ta gano lamarin ne a cikin wani sako da hadimin gwamna Radda, Ibrahim Kaulaha Muhammad ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Borno: Manya na ci gaba da zuwa jaje Maiduguri, an ƙara bada tallafin N50m

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Radda ya ba mutanen Maiduguri N100m

Gwamna Dikko Umaru Radda ya mika kudi N100m ga al'ummar jihar Borno saboda rage raɗaɗin ambaliyar ruwa.

Yayin mika kudin, gwamna Dikko Umaru Radda ya ce ya mika su ne a madadin dukkan al'ummar jihar Katsina.

Radda ya yi addu'a ga mutanen Maiduguri

Gwamna Radda ya ce ambaliyar ruwan na cikin jarrabawa mafi muni da suka faru ga al'ummar Maiduguri.

Saboda haka ya yi addu'ar Allah ya kare mutanen Maiduguri da kuma kare dukkan Najeriya daga irin jarrabawar.

Zulum ya yi godiya ga gwamna Radda

Yayin jawabi, gwamna Babagana Umara Zulum ya yi godiya ga gwamnatin jihar Katsina bisa tunawa da su da suka yi bayan shiga jarrabawa.

Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce wannan ya nuna hadin kai da son juna da ke tsakanin yan Najeriya musamman a lokacin tsanani.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Yan majalisar dattawa sun ziyarci Borno, sun mika tallafin N74m

Majalisa ta ba Maiduguri tallafin kudi

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar wakilai ta bi sahun Sanatocin majalisar dattawa da yan siyasa a kasar nan wajen kai gudunmawa ga gwamnatin jihar Borno.

Daidaikun jama'a da yan siyasa sun tashi haikan wajen mika tallafi ga gwamna Babagana Umara Zulum domin taimakon wadanda ambaliya ta shafa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng