"Mu na Nemansa": EFCC Ta Yi Martani kan Mika Wuyan Yahaya Bello, Ta Fadi Yadda Ake ciki

"Mu na Nemansa": EFCC Ta Yi Martani kan Mika Wuyan Yahaya Bello, Ta Fadi Yadda Ake ciki

  • Hukumar EFCC ta yi martani kan rade-radin cewa tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya mika kansa gare ta
  • EFCC ta ce har zuwa wannan lokaci tana cigaba da neman Yahaya Bello ruwa a jallo bayan shafe watanni suna wasan buya
  • Wannan na zuwa ne bayan zargin badakalar makudan kudi har N80.2bn da ake zargin tsohon gwamnan lokacin mulkinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Hukumar yaki da cin hanci (EFCC) ta yi magana kan dambarwar Yahaya Bello da ake ciki.

Hukumar ta ƙaryata cewa Yahaya Bello ya mika kansa gare ta inda ta ce tana nemansa ruwa a jallo.

EFCC ta yi magana kan rade-radin cewa Yahaya Bello ya mika wuya
Hukumar EFCC ta nisanta cewa Yahaya Bello na hannunta. Hoto : Economic and Financial Crimes Commission.
Asali: Twitter

EFCC ta magantu kan batun Yahaya Bello

Kara karanta wannan

An firgita da jin harbe harbe da EFCC suka farmaki Yahaya Bello a Abuja

EFCC ta fayyace hakan ne da yammacin yau Laraba 18 ga watan Satumbar 2024 a shafinta na Instagram.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar ta ce har yanzu tana neman tsohon gwamnan kan zargin karkatar da makudan kudi har N8.2bn.

Kakakin hukumar, Dele Oyewale ya tabbatar da cewa maganar cewa Yahaya Bello ya mika kansa kanzon kurege ne.

"Rahotanni daga gidajen jaridu sun yada cewa tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello yana hannun hukumar EFCC, wannan ba gaskiya ba ne."
"Hukumar tana mai tabbatar da cewa Yahaya Bello ba ya tare da ita, kuma har yanzu tana nemansa ruwa a jallo kan zargin badakalar N80.2bn."

- Dele Oyewale

Ana yada Yahaya Bello yana hannun EFCC

Wannan na zuwa ne bayan yada rade-radin cewa Yahaya Bello ya mika kansa ga hukumar EFCC ba tare da wata gardama ba.

Kara karanta wannan

PDP ta gaji da lamarin gwamnan Sokoto, ta bukaci EFCC ta binciki N30bn da ya ware

Sai dai daga bisani wasu rahotanni suka ce hukumar ta fadi yadda aka yi Yahaya Bello ya shiga hannunta kafin daga bisani ta ƙaryata.

Yahaya Bello dai ana zarginsa da handame makudan kudi har N80bn tun bayan barinsa kujerar gwamna a jihar Kogi kafin mika mulki ga Gwamna Usman Ododo.

EFCC ta magantu kan cafke Yahaya Bello

Mun kawo labarin cewa tsohon gwamnan jihar Kogi ya shiga hannun jami'an hukumar EFCC bayan kwashe lokaci mai tsawo suna wasan ɓuya.

Majiyoyi a hedkwatar hukumar sun bayyana cewa jami'an EFCC ne suka cafke Yahaya Bello ba amsa gayyatar hukumar ya yi ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.