Sanata Abbo Ya Fadi Abin da Zai Yi kan Zargin Lalata da Matar Aure, Ya ba Ta Wa'adi

Sanata Abbo Ya Fadi Abin da Zai Yi kan Zargin Lalata da Matar Aure, Ya ba Ta Wa'adi

  • Tsohon sanatan Adamawa ta Arewa, Elisha Abbo ya sha alwashin daukar mataki kan zargin lalata da ake yi masa
  • Abbo ya bukaci Wange David da ta janye kalamanta tare da neman yafiya cikin awanni 72 kacal ko abin ya girmama
  • Wannan na zuwa ne bayan David ta zargi Abbo da sakin bidiyonsu da suke lalata guda daga cikin 32 da suka ɗauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Adamawa - Tsohon sanata a jihar Adamawa, Elisha Abbo ya magantu kan zargin lalata da ake yi masa.

Elisha Abbo ya ce zai dauki matakin shari'a kan Wange David game da faifan bidiyon lalata da ita.

Kara karanta wannan

Yadda mutane sama da 100 su ka rasu a manyan iftila'I 4 a Arewacin Najeriya

Sanata Abbo zai dauki matakin shari'a kan matar aure saboda zargin lalata
Sanata Elisha Abbo ya bukaci neman tafiyarsa daga matar aure da take neman bata masa suna. Hoto: Senator Elisha Abbo.
Asali: Facebook

Sanata Abbo zai maka matar aure a kotu

Sanatan da ya wakilci Adamawa ta Arewa tuni ya musanta zargin inda ya ce an yi domin bata masa suna, cewar rahoton Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kwanakin baya ne, David ta zargi sanatan da sakin bidiyonsu suna lalata daga cikin 32 da suka nada, Punch ta ruwaito hakan.

Lauyan sanatan, Odiyowvi Osusu ya zargi David ta batawa Abbo suna ta kowane bangare da kuma ba da bayanai da suka na karya ga al'umma.

Sanata ya ba matar aure wa'adin awa 72

Osusu ya bukaci matar da ta nemi yafiyar Abbo cikin awanni 72 a gidan talabiji sannan a wallafa a manyan jaridu guda uku.

Sannan Osusu ya ce dole a yada bayanan nata na yafiya a inda ta yi hira domin wanke kansa.

Kara karanta wannan

Kotu ta sake zama kan zargin tsohon Minista a Kebbi da dirkawa budurwa ciki

Ya ce kin bin wannan umarni zai tilasta su maka ta a kotu domin neman hakkin sanata saboda bata masa suna da aka yi.

Sanata Abbo ya magantu kan bidiyon lalata

Kun ji cewa Sanata Ishaku Abbo, haifaffen jihar Adamawa ya sake jawo ce-ce-ku-ce a kafofin sada zumunta bayan bullar wani bidiyo a baya-bayan nan.

A cikin faifan bidiyon an ga wani mutumi da ake zargin Sanata Ishaku Abbo ne yana lalata da wata mata da ake zargin matar aure ce.

Sai dai tsohon sanatan ya musanta wannan zargi inda ya ce ba shi ne mutumin da ke cikin bidiyon ba tare da yin karin haske a kan lamarin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.