NNPCL Ya Fadi Lokacin da Matatar Man Gwamnati Za Ta Fara Aiki Gadan Gadan

NNPCL Ya Fadi Lokacin da Matatar Man Gwamnati Za Ta Fara Aiki Gadan Gadan

  • Kamfanin man Najeriya na NNPCL ya yi bayani kan korafin da yan kasa ke yi game da matatun man gwamnati musamman na Fatakwal
  • NNPCL ya ce ba gazawa ba ce ko rashin shiri ya saka matatar man Fatakwal gaza fara aiki sai dai kawai akwai shirye shiryen da suke yi ne
  • Haka zalika kamfanin kamfanin NNPCL ya bukaci al'ummar Najeriya, musamman yan jarida su rika tantance bayanai kafin yada su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kamfanin man Najeriya ya fitar da bayani kan matatar man gwamnatin tarayya da ke Fatakwal.

NNPCL ya ce matatar man ba ta gaza aiki ba ne saboda rashin shirin gwamnatin sai dai akwai wasu dalilai na daban.

Kara karanta wannan

Rikicin farashi: Yan kasuwa sun gaza samun man Dangote daga NNPCL

Mele Kyari
NNPCL ya yi bayani kan matatar man Fatakwal. Hoto: NNPC Limited.
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa kamfanin ya bukaci yan jarida su rika tantance labaran da suke yaɗawa a kan harkokin man fetur.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe za a bude matatar man gwamnati?

A yayin wani taro na ba yan jarida horo, jami'in NNPCL, Solomon Oseagah ya ce matatar Fatakwal tana tace mai a halin yanzu.

Sai dai Solomon Oseagah ya ce ba a fitar da sanarwa ba ne kan kaddamar da matatar saboda shirin da NNPCL ke yi na ganin an kammala komai kafin sanar da jama'a.

Haka zalika, Oseagah ya tabbatar da cewa kafin karshen shekarar da muke ciki shugaba Bola Tinubu zai kaddamar da matatar gwamnati da ke Fatakwal.

NNPCL ya nemi adalci wajen yan jarida

Kamfanin mai na NNPCL ya bukaci masu harkar yada labarai da su rika masa adalci yayin haɗa rahoto a kan man fetur da sauransu.

Kara karanta wannan

NNPC ya bayyana dalilin da ya sa 'yan kasuwa ba za su iya sayen man Dangote ba

NNPCL ya ce yana da kyau yan jarida su rika tantance dukkan abin da za su yada idan ya shafi kamfanin domin kaucewa yada labari maras tushe.

The Guardian ta wallafa cewa Solomon Oseagah ya tabbatar da cewa kamfanin NNPCL ba ya takun saƙa da matatar Dangote ta kowane bangare.

IPMAN ta koka kan samun man Dangote

A wani rahoton, kun ji cewa yan kasuwar man fetur sun ce sabani da aka samu kan farashi na cikin dalilan da suka sa NNPCL bai ba su mai din Dangote ba.

Shugaban kungiyar IPMAN, Abubakar Maigandi ya ce an shiga rashin tabbas kan jigilar fetur duk da an fara tace shi a gida Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng