Yadda Mutane Sama da 100 Su ka Rasu a Manyan Iftila'i 4 a Arewacin Najeriya

Yadda Mutane Sama da 100 Su ka Rasu a Manyan Iftila'i 4 a Arewacin Najeriya

Mazauna Arewacin kasar sun fuskanci kalubale da dama da su ka haddasa asarar rayuka kusan 100 a jihohin Kaduna, Zamfara, Borno da Bauchi a kasa da mako biyu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Ambaliyar ruwa da aka wayi garin Talata da ita, da wata ambaliyar da aka samu a jihar Bauchi sun salwantar da rayukan jama'a da dama.

Iftila'i
Mutane sama da 100 sun rasu a iftila'in a Arewacin kasar nan Hoto: The Governor of Borno State/Uba Sani
Asali: Facebook

Legit ta tattaro wasu daga cikin manyan iftila'i hudu da aka samu a kasa da mako biyu a Arewa, da halin da ake ciki a yanzu.

Masifun da suka auku a Arewacin Najeriya

1. Ambaliyar Bauchi ta kashe mutane 24

Kara karanta wannan

Ambaliya: Dattijon attajiri, Dantata ya tallafa wa Borno da sama da Naira biliyan 1

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Talata ne aka samu ambaliya a jihar Bauchi da ta yi sanadin rasuwar mutane akalla 24, kamar yadda gwamnatin Bauchi ta wallafa a shafinta na yanar gizo.

Gwamnatin jihar, karkashin Bala Mohammed a ranar Laraba ta bayyana cewa an fara shirin taimakon mutanen da su ka fada matsala sakamakon iftila'in, har an kafa kwamiti kan batun.

2. Yadda ambaliya ta mamaye Borno

Watakila saboda girman iftila'i da yadda ruwa ya mamaye fiye da Maiduguri a ranar Talata ya sa na Bauchi ya dan lafa, domin ambaliya ce irinta ta farko a cikin shekaru 30 a Maiduguri.

A halin da ake ciki, gwamnatin Babagana Zulum na samun tallafin ambaliya daga masu kudi da gwamnatocin kasar nan bayan rasuwar mutane akalla 37.

3. Hadarin maulidin Kaduna

Biyo bayan shiga watan Rabi'ul Auwal, musulmi sun fara tafiye-tafiye domin halartar maulidin fiyayyen halitta Annabi Muhammadu SAW a ciki da wajen jihohinsu, kuma a irin wannan ne aka samu mummunan hadari a Kaduna.

Kara karanta wannan

Ambaliyar Maiduguri: Mutanen da aka ceto daga gidaje sun haura 3,600

Mutum sama da 40 ne su ka rasu a hanyarsu ta zuwa Saminaka domin taron maulidi, lamarin da gwamnan jihar, Uba Sani ya mika ta'aziyya tare da daukar alkawarin tallafa wa wanda abin ya rutsa da su.

4. Kifewar jirgin Zamfara ya jawo asarar rayuka

Ba a gama jimamin iftila'in da ake fuskanta ba sai jirgin ruwa ya kife a Rafin Mashaya karamar hukumar Gummi a jihar Zamfara.

An yi nasarar ceto wasu mutane biyar da rai, yayin da ake neman gawarwakin wasu mutane tare, lamarin da ya kara jefa jama'a cikin alhini.

Ambaliya: Tinubu ya kafa asusun taimako

A wani labarin kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana kafa asusun da za a tallafa wa mutanen da iftila'in ambaliya ya rutsa da su a jihar Borno.

Shugaban, wanda ya samu rakiyar manyan mukarraban gwamnati, ya nemi masu kudin kasar nan da sauran masu kishi su agaza wa mutanen da su ka fada cikin iftila'in.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.