Rikicin Farashi: Yan Kasuwa Sun Gaza Samun Man Dangote daga NNPCL
- Yan kasuwar man fetur sun ce sabani da aka samu kan farashi na cikin dalilan da suka sa NNPCL bai ba su mai din Dangote ba
- Shugaban kungiyar IPMAN, Abubakar Maigandi ya ce an shiga rashin tabbas kan jigilar fetur duk da an fara tace shi a gida Najeriya
- A ranar Lahadi ne kamfanin NNPCL ya fara daukar tataccen man fetur daga matatar Dangote da ke jihar Legas zuwa jihohi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kwanaki uku bayan daukar fetur daga matatar Dangote yan kasuwa sun gaza samun man daga NNPCL.
Rahotanni sun nuna cewa rashin samun daidaito kan farashin man feturin ne ya kawo tsaiko a kan lamarin.
Jaridar Business Day ta wallafa cewa wani dillalin man fetur, Muhammad Lawal ya koka kan rashin samun man fetur din.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NNPCL ya dauki mai daga matatar Dangote
A ranar Lahadi kamfanin man fetur na NNPCL ya fara daukar man fetur a matatar Dangote da ke Legas.
Bayanai sun nuna cewa kamfanin NNPCL ne zai dauki man fetur da aka tace daga matatar Dangote domin raba shi ga yan kasuwa a Najeriya.
Yan kasuwa sun gaza samun man fetur
Shugaban kungiyar IPMAN, Abubakar Maigandi ya ce har yanzu ba su samu man da NNPCL ya dauka daga matatar Dangote ba.
Haka zalika wani babban 'dan kasuwar a harkar man fetur, Muhammad Lawal ya ce kwanaki uku da daukar man amma ya gaza iso yan kasuwa.
Me ya hana yan kasuwa samun man fetur?
Shugaban kungiyar IPMAN, Abubakar Maigandi ya ce rashin samun daidaito kan farashi ne ya hana su samun man.
Abubakar Maigandi ya ce rashin samun man ya jefa harkar jigilar man fetur cikin ruɗani a fadin Najeriya.
Farashin fetur: SERAP ta kai Tinubu kara
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar kare hakkokin tattalin arziki (SERAP) ta maka Shugaba Bola Tinubu a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Kungiyar SERAP ta shigar da Tinubu da ministan shari'a, Mista Lateef Fagbemi da kuma NNPCL kan karin kudin man fetur a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng