Sojoji Sun Bude Wuta, An Damke Masu Taimakawa 'Yan Bindigan Arewa da Makamai
- Dakarun sojojin kasar nan sun yi nasara kan masu kai makamai ga yan ta'adda a daji a hanyarsu ta mika wasu mugayen makamai
- Mutanen da ba a fadi adadinsu ba sun shiga hannu a jihar Filato inda aka gano wasu makamai da alburusai masu tarin yawa a wajensu
- Kamen na zuwa ne kwanaki bayan wasu yan bindiga da sojoji su ka koro su ka kashe mutane biyar a wani kauye da ke Bokkos a Filato
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Plateau - Dakarun sojan kasar nan na rundunar 'Operation save heaven' sun cafke rikakkun masu safarar makamai ga yan ta'adda.
An kama wadanda ake zargin 'yan aiken yan ta'addan a yankin Bayamemi da ke karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato.
Zagazola Makama, fitaccen mai sharhi ka harkokin tsaro ne ya tabbatar da aikin dakarun a shafinsa na X a makon nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar ta ce majiyoyi daga rundunar tsaron kasar nan ne su ka bayyana masa lamarin.
An kama miyagun makamai daga 'yan bindiga
Jaridar The Guardian ta wallafa cewa jami'an tsaro sun kwato bindigu kirar Ak-47 da harsasan makamin guda 47.
Karin makaman da aka samu sun hada da dubbunnan harsashi na bindigu kira daban-daban, da karin bindiga kirar FN.
Halin da yan aiken 'yan bindiga ke ciki
Rahotanni na cewa yanzu haka mutanen da aka damke hade da miyagun makaman da aka samu a hannunsu na wajen rundunar sojan kasar nan.
Ana ci gaba da binciken mutanen da ba a sanar da adadinsu ba kafin daukar mataki na gaba na dakile ta'addanci da safarar makaman.
Yan bindiga sun kashe matasa a Filato
A baya kun ji cewa wasu miyagun yan ta'adda sun kai hari kan matasa a hanyarsu ta dawowa kauyensu na Mbar da ke karamar hukumar Bokkos, tare da kashe mutane biyar.
Shugaban ci gaban yankin, Mista Farmasun Fuddanga da ya tabbatar da lamarin ya koka da yadda jami'an tsaro su ka yi jinkirin kawo masu dauki, har aka kashe matasan su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng