Wahalhalu Sun Tsananta a Najeriya, Abdulsalami Ya ba Tinubu Muhimmiyar Shawara
- Janar Abdulsalami Abubakar ya tunatar da Shugaba Bola Tinubu cewa 'yan Najeriya na kara fuskantar tsananin wahalar rayuwa
- Tsohon shugaban kasar ya ce yunwa, tsadar rayuwa da tsadar fetur da ake fuskanta a kasar nan na neman su wuce gona da iri
- A yayin da ya ba gwamnati shawarar abin da ya kamata ta yi, Abdulsalami ya ce raba tallafin abinci ba zai magance matsalar ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Neja - Tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar yayi wa shugaba Bola Ahmed Tinubu magana kan kuncin rayuwa.
Janar Abdulsalam Abubakar ya koka cewa yunwa, tsadar rayuwa da matsin tattali a kasar na ci gaba da tabarbarewa inda suke neman 'wuce gona da iri.'
Jaridar The Cable ta rahoto cewa Abdulsalami ya bayyana hakan a Minna, jihar Neja a lokacin da bakunci kungiyar CDHR, bisa jagorancin Abdullahi Mohammed Jabi a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Walhalu sun tsananta' - Janar Abdulsalami
Tsohon shugaban kasar ya yi takaicin yadda 'yan Najeriya ke gaza biyan bakatunsu na yau da kullum kamar abinci da zirga zirga duk da fadi tashin da suke yi.
Abdulsalami ya bayyana cewa:
"Kowa na korafi a kan tsadar rayuwa, kuma da alama lamarin na son wuce gona da iri. Mutane a yanzu ba sa iya cin abinci sau uku a rana.
"Sufuri ya yi tsada saboda tsadar mai, an kara kudin makarantu ga kuma uwa uba rashin kudi a hannun jama'a wanda ya jefa su a cikin mawuyacin hali."
Abdulsalami ya ba Tinubu shawara
Tsohon shugaban kasar ya ce yana daga cikin kwamitin da suka mikawa gwamantin tarayya jadawalin magance matsalar tattalin arziki, amma shiru har yanzu.
Ya ce dabi'ar da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta dauka na raba tallafin kayan abinci ba zai magance hauhawar farashin kayan masarufi a kasar ba.
Abdulsalami ya ba Tinubu shawarar cewa gwamnatinsa ta sayi kayan abinci da na masarufi ta sayar da su a farashi mai rasu ta yadda talakan kasar zai iya saye, a cewar rahoton SaharaReporters.
Abdulsalmi ya yi gargadi kan zanga-zanga
A yayin da ake shirin fuskantar wata zanga zangar a fadin kasar nan kan adawa da gwamnatin Tinubu, Abdulsalami ya gargadi masu shirya zanga-zangar.
Abdulsalami ya ce akwai bukatar a yi lura da barnar da aka yi a zanga zangar da ta gabata, a kuma auna abin da ka iya zuwa ya dawo a zanga zangar 1 ga Oktoba da ake shirin yi.
Ya koka kan cewa zanga zangar da ta gabata ta haifar da satar dukiya da lalata kadarorin jama'a kuma an samu asarar rayuka a abin da ya kamata ya zama na lumana.
Shugaba Tinubu ya gana da Abdulsalami
A 2023, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya sanya labule da tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar.
Ganawar Janar Abdulsalami da shugaban kasar na zuwa ne 'yan kwanaki kadan bayan da aka rantsar da Tinubu a matsayin shugaban Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng