Ambaliyar Ruwa: Aminu Ado Bayero Ya Jajantawa Mutanen Borno, Ya Yi Addu'a

Ambaliyar Ruwa: Aminu Ado Bayero Ya Jajantawa Mutanen Borno, Ya Yi Addu'a

  • Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Bayero ya jajantawa mutanen jihar Borno kan ambaliyar ruwan da ta auku
  • Mai martaba Sarkin ya nuna kaɗuwarsa kan lamarin wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa
  • Ya kuma miƙa saƙon jaje ga shugaban ƙasa Bola Tinubu, Gwamna Babagana Umara Zulum da Shehun Borno

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya nuna alhininsa kan ambaliyar ruwan da ta auku a jihar Borno.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya jajantawa al’ummar jihar Borno dangane da iftila’in ambaliyar ruwan wanda ya raba mutane da dama da matsugunansu.

Aminu Ado Bayero ya yi alhini kan ambaliyar ruwa
Aminu Ado Bayero ya jajantawa mutanen Borno kan ambaliyar ruwa Hoto: Masarautar Kano
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi jajen ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun babban sakataren yaɗa labaransa, Abubakar Balarabe Kofar Naisa.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Dattijon attajiri, Dantata ya tallafa wa Borno da sama da Naira biliyan 1

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Aminu Ado ya ce kan ambaliyar ruwa?

Mai martaba Sarkin ya ce ambaliyar wani lamari ne mai ban tausayi wanda ya ratsa zuƙatan mutanen ƙasar nan baki ɗaya.

"Duk da cewa irin wannan lamari ba kasafai yake aukuwa ba, amma idan ya zo ba mu da wata mafita face mu koma ga Allah mu nemi taimakonsa tare da yin addu’a ka da ya sake aukuwa a nan gaba."
"Muna ddu’ar Allah ya ji kan waɗanda suka rasa rayukansu, Ya ba waɗanda suka samu raunuka sauƙi sannan Ya mayar da abin da ya fi alkhairi ga waɗanda suka rasa dukiyoyinsu."

- Alhaji Aminu Ado Bayero

Sarki Aminu Ado Bayero ya kuma jajantawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, Gwamna Babagana Umar Zulum da Shehun Borno, Alhaji Mustapha El Garbi.

Atiku ya ba da gudunmawa a Borno

Kara karanta wannan

Ambaliyar Maiduguri: Shugaba Tinubu zai nema wa jama'a taimako, ya kafa asusun tallafi

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya kai ziyarar jaje a Maiduguri saboda ambaliyar ruwa.

Atiku Abubakar ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 100 domin tallafawa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng