Bayan Zargin 'Tatsar' Yan Kasuwa, Hukumar Kwastam Ta Fara Binciken Jami'anta a Kano

Bayan Zargin 'Tatsar' Yan Kasuwa, Hukumar Kwastam Ta Fara Binciken Jami'anta a Kano

  • Hukumar kwastam shiyyar Kano da Jigawa ta tabbatar da samun koken yan kasuwar Abubakar Rimi kan jami'anta
  • Kakakin hukumar da ke kula da shiyyar, Nura Abdullahi ya ce tuni aka fara bincike domin gano wadanda ake zargi
  • An samu korafe-korafe daga yan kasuwar inda su ka zargi jami'an da tilasta masu biyan miliyoyi kafin dauke kayansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Yan kasuwar Abubakar Rimi da aka fi sani da kasuwar Sabon Gari a Kano sun yi korafi kan tilasta masu biyan makudan kudade da jami'an kwastam ke yi.

Jami'in hulda da jama'a na yan kasuwar Sabon Gari, Nazifi Auwalu ya ce jami'an kwastam sun sanya tsoro a zukatansu.

Kara karanta wannan

Jama'a sun razana bayan jami'ai da bindigu sun yi awon gaba da kantoma a Kano

Kwastam
Ana zargin jami'an a Kano ta tilasta karbar cin hanci Hoto: @CustomsNG
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Nazifi Auwalu ya ce yan kasuwa ba sa iya fitar da kayansu zuwa wasu wuraren saboda 'harajin' da jami'an kwastam ke tilasta su biya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Miliyoyi jami'an kwastam ke karba" - Yan kasuwa

Wani dan kasuwar Sabon Gari, ya ce jami'an kwastam sun tilasta masa biyan Naira Miliyan biyu lokacin da ya kai kaya Kaduna.

A bangarensa, Nazifi Auwalu, kakakin yan kasuwar ya ce ba a jima da kwace mota da ta dauko masa turare ba, kuma ba a sake ta ba sai da ya biya Naira Miliyan daya.

Kwastam ta fara binciken jami'anta

Hukumar kwastam ta kasa ta bayyana cewa ta samu labarin zargin tilasta biyan cin hanci da wasu jami'anta ke yi wa yan kasuwa a Kano.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar shiyyar Kano da Jigawa, Nura Abdullahi ya ce tuni aka fara binciken zargin, kuma za a hukunta duk wanda aka kama da laifi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga da akidar Boko Haram sun shigo Sakkwato daga kasar waje sun kafa daula

An kashe jami'in kwastam

A baya mun ruwaito yadda wani jami'in kwastam ya gamu da karshensa lokacin da ya ke bakin aiki a hannun dan fasa kwaurin da ake kokarin kama wa a Jigawa.

Mutumin da ake zargin dan fasa kwauri ne ya bankade IC Hamza Abdullahi Elenwo da motarsa a ranar Juma'a, a kokarin tsere wa kar jami'an kwastam su kama shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.