"Kin Koyi Rayuwa": Gwamna Ya Fadi Yadda Aka Zalunci Ƴarsa a Sansanin NYSC
- Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya bayyana yadda ƴarsa ta sha wahala a sansanin horas da matasa masu bautar ƙasa
- Mista Makinde ya ce ya yi mamaki yadda ta iya shafe makwanni uku bayan ta ce masa kwana ɗaya kawai za ta yi sansanin
- Gwamnan ya shawarci matasa da su yi amfani da damar wurin gina rayuwarsu inda ya ce shekaru 34 da suka wuce shi ma yana wannan matsayi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Oyo - Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya shawarci matasa masu bautar ƙasa kan jajircewa a rayuwa.
Gwamnan ya ce a wannan lokaci da suke ciki wata dama ce da wasu za su samu hanyar cigaban rayuwarsu.
NYSC: Gwamna Makinde ya shawarci masu bautar kasa
Punch ta ce Makinde ya fadi haka ne ta bakin hadiminsa, Suleiman Olanrewaju yayin jawabi ga matasan a yau Talata 17 ga watan Satumbar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan wanda yarsa ke cikin wadanda suka kammala samun horaswa ya bukace su da suyi amfani da wannan dama.
Ya shawarce su da ka da su yi wasa da damar saboda za ta iya zama hanyar bunkasa rayuwarsu, cewar rahoton Tribune.
"Ina son fitar da abubuwa guda biyu, na farko ƴata tana nan tare da ku wanda ke nuna mu ma shugabanninku mutane ne kamar ku."
"Na biyu, mu ma muna fuskantar abin da kuke ciki kamar yadda iyayenku suke fuskanta."
"Da nake magana da wakilan gwamnan jihar Lagos, na ce na yi mamaki ƴata za ta iya zama har na tsawon makwanni uku saboda ta ce kwana ɗaya za ta yi."
- Seyi Makinde
Gwamnan Oyo ya yabawa ƴarsa a sansanin NYSC
Makinde ya ce wasu sun zalunci ta sosai a lokacin da take sansanin inda ya ce haka ake koyon rayuwa.
"Ta ce mani ta ji dadin zama a sansanin duk da wasu sun zalunce ta sosai, na ce mata barka da zuwa rayuwa ta gaskiya ba tare da kariya ba inda dole ki yi abin da kowa yake yi."
- Seyi Makinde
Gwamna Makinde ya musanta ikirarin Tinubu
A baya kun ji cewa Gwamna Seyi Makinde ya musanta ikirarin Bola Ahmed Tinubu na rabawa jihohi N570bn domin rage raɗaɗin kuncin rayuwa.
Tun farko shugaban ƙasa ya ce gwamnatinsa ta rabawa gwamnoni maƙudan kuɗi domin su faɗaɗa shirye-shiryen tallafawa ƴan Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng