"An Karya Doka," An Taso NNPC a Gaba kan Farashin Man Fetur na Matatar Ɗangote
- Babban lauya a Najeriya kuma mai fafutukar kare hakkin ɗan adam, Femi Falana SAN ya caccaki kamfanin NNPCL
- Falana SAN ya ce ƙayyade farashin man da kamfanin NNPC ya yi ya saɓawa sashi na 205 na dokar man fetur PIA
- Wannan na zuwa ne bayan kamfanin mai ya fara jigilar fetur daga matatar Ɗangote ranar Lahadin da ta gabata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Fitaccen lauyan nan ɗan fafutukar kare haƙƙin ɗan adam, Femi Falana (SAN), ya yi magana kan farashin man feturin matatar Ɗangote.
Falana ya bayyana cewa a tsarin doka, haramun ne kamfanin mai na kasa NNPCL ya tsoma baki ko ya tsaida farashin man fetur da matatar Ɗangote ta tace.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Femi Falana ya fitar ranar Talata, 17 ga watan Satumba, 2024, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NNPCL ya saɓawa tanadin dokar PIA
Bisa haka Falana ya ce yanke farashin man Ɗangote da NNPCL ya yi ya saɓawa tanadin sashi na 205 na dokar man fetur PIA.
Lauyan ya ce:
"Ranar 5 ga watan Satumba, NNPC ya fito ya sanar da cewa matsalar canjin kuɗin waje ne ya kawo tashin farashin man fetur kamar yadda dokar PIA ta tanada.
"Mataimakin shugaban sashen harkokin mai na NNPC, Mr. Adedapo Segun da kansa ya ce sashe na 205 a PIA ya tanadi cewa yanayin kasuwa ne ke ƙayyade farashin mai.
"A cewarsa, an maida komai hannun ƴan kasuwa ma'ana babu ruwan gwamnati ko kamfanin NNPC wajen yanke farashin litar fetur."
Falana ya faɗi dokar da NNPCL ya karya
Femi Falana ya ƙara da cewa NNPCL ya yi tufka da warwara, ya fito ya sanar da farashin da za a sayar da man feturin matatar Ɗangote.
Ya ce abin da NNPCL ya yi na ƙayyaɗe farashin ya saɓawa sashi na 205 na dokar PIA, wanda ya ce a bar yanayin kasuwa ya ƙayyade farashin litar man fetur.
Kalaman babban lauyan na zuwa ne bayan kamfanin mai ya fara jigilar fetur daga matatar Ɗangote ranar Lahadi a cewar rahoton Daily Post.
Yan kasuwa na shirin tsallake matatar Ɗangote
A wani rahoton kuma dillalan mai sun bayyana cewa fetur din da matatar Dangote ta tace ya yi matukar tsada a kasuwa.
Wannan ta sa yan kasuwar su ka fara tunanin fara sayo man fetur da kudinsu kai tsaye daga kasashen wajen zuwa kasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng