Jami'an Tsaro Sun Samu Nasara kan 'Yan Bindiga a Jihar Neja
- Jami'an tsaro na hukumar DSS sun samu nasarar hallaka ƴan bindiga mutum biyu a wani samame da suka kai a jihar Neja
- An kuma cafke wasu mutane da dama da ake ƴan bindiga a yayin samamen da suka kai a wani ƙauye da ke ƙaramar hukumar Tafa
- Majiyoyi sun bayyana cewa an kai samamen ne a wata rugar makiyaya da ke kusa da ƙauyen Hayin-Nasara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Neja - Jami'an tsaro na hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) sun hallaka ƴan bindiga mutum biyu a jihar Neja.
Jami'an tsaron na DSS sun kuma cafke wasu da dama da ake zargin ƴan bindiga ne a wani samame da suka kai a ƙauyen Hayin-Nasara da ke ƙaramar hukumar Tafa ta jihar.
Yadda jami'an tsaro suka kashe ƴan bindigan
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa jami'an na DSS sun kai samamen ne a ranar Juma'a a wata rugar makiyaya da ke kusa da ƙauyen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya a ƙauyen Hayin-Nasara ta bayyana cewa a yayin samamen an gano wani buhu ɗauke da kuɗaɗe da bindigu a cikin wata bukka.
"Nan da nan muka garzaya zuwa wajen inda muka ga gawar ɗaya daga cikin mutum biyun da ake zargi, yayin da ɗaya gawar ta wani da ake kira 'pointer' jami'an tsaron suka tafi da ita."
- Wata majiya
Wani ɗan banga a yankin ya bayyana cewa waɗanda ake zargin da aka cafke sun kwashe shekaru suna zaune a wajen, yayin da wasu ba su daɗe da dawowa wajen ba domin samun mafaka sakamakon takura musu da aka yi a daji.
"Daga baya tawagar wasu sojoji daga Abuja sun zo sun ƙona da yawa daga cikin bukkokinsu."
- Wani ɗan banga
Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, kan lamarin ya ce bai samu rahoto a kai ba.
Kakakin ya ƙara da cewa har yanzu rundunar ba ta samu wasu bayanai ba kan batun.
Ƴan bindiga sun kai hari a coci
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun kai farmaki wuraren ibadar mabiya addinin kirista watau coci-coci a kauyen Bakinpah-Maro, ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun hallaka aƙalla mutum uku, sannan suka yi awon gaba da wasu da dama a yayin harin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng