"Zai Iya Shiga Kotu": Rundunar Tsaro Ta Yi Gargadi kan Dambarwar Seamnan Abbas Haruna

"Zai Iya Shiga Kotu": Rundunar Tsaro Ta Yi Gargadi kan Dambarwar Seamnan Abbas Haruna

  • Yayin da ake ta cece-kuce kan dambarwa game da sojan ruwa, Seaman Abbas Haruna, rundunar tsaro ta yi magana
  • Rundunar ta bukaci al'umma da su guji magana kan lamarin har sai an kammala bincike da ake yi a kai
  • Wannan na zuwa ne bayan zargin Burgediya janar MS Adamu da cin zarafin Abbas Haruna na tsawon shekaru shida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Rundunar tsaron Najeriya ta yi magana kan dambarwa game da sojan ruwa, Abbas Haruna.

Rundunar ta gargadi al'umma kan cigaba da fadin albarkacin bakinsu ba tare da jiran matakan hukumar ba.

Rundunar tsaro ta gargadi al'umma gaje yada hotunan MS Adamu kan zargin cin zarafin Abbas Haruna
Rundunar tsaro ta ba da tabbacin bincike tare da yin adalci game da sojan ruwa, Abbas Haruna. Hoto: Brekete Family.
Asali: Facebook

Seamnan Abbas Haruna: Rundunar tsaro ta yi gargadi

Kara karanta wannan

Seaman Abbas: Muhimman abubuwa 7 a labarin sojan ruwan da ya ja hankalin ƴan Najeriya

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran hukumar, Tukur Gusau ya wallafa a shafinta na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta bukaci al'umma da su guji wallafa hoton Burgendiya janar MS Adamu saboda kare masa hakkinsa.

Hukumar ta ba al'ummar Najeriya tabbacin cewa za ta yi bincike na gaskiya tare da sanar da su matakin gaba.

Rundunar tsaro ta fadi matakin da ake kai

"Ana ta yada hotunan Burgediya janar MS Adamu kan alaka da abin da ya faru da sojan ruwa, Abbas Haruna."
"Hotunan Burgediya janar MS Adamu da ake yadawa ba shi da alaka da dambarwar da ta shafi sojan ruwa, Abbas Haruna."
"Hukumar tsaro tana kira ga al'umma su bari kwamitin da hafsan tsaro, Janar Christopher Musa ya kafa ya yi aikinsa."
"Muna rokon al'umma su guji magana kan lamarin saboda wanda ake magana a kansa yana da cikakken yancin shiga kotu saboda wallafa hotunansa babu ka'ida."

Kara karanta wannan

Seaman Abbas: Dattawan Arewa sun yi tofin Allah tsine kan zargin zaluntar sojan ruwa

- Cewar sanarwar

Rundunar ta ba yan Najeriya tabbacin cigaba da bin doka da oda tare da tabbatar da yin adalci a binciken domin daukar mataki.

Seamnan Abbas: Dattawan rewa sun yi gargadi

Kun ji cewa Kungiyar Northern Elders Forum ta bayyana takaicin labarin cin zarafin wani jami'in rundunar sojan ruwa, Seaman Abbas Haruna.

Jami'in hulda da jama'a a NEF, AbdulAzeez Suleiman ya ce yadda aka samu labarin Husaina Iliyasu kan cin zarafin mijinta ya jawo damuwa.

Sanarwa da AbdulAzeez Suleiman ya fitar, ta ce lamarin ya jawo tambayoyi kan gwadaben tafiyar da jami'an rundunar tsaron.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.