'Ka da Mu Zargi Kowa': Tinubu Ya Bayyana Abin da Ya Jawo Ambaliyar Maiduguri

'Ka da Mu Zargi Kowa': Tinubu Ya Bayyana Abin da Ya Jawo Ambaliyar Maiduguri

  • Shugaba Bola Tinubu ziyarci babban birnin Borno inda ya sanar da asusun bayar da agaji ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa
  • Tinubu ya ce ambaliyar Maiduguri mukaddari ce daga Allah don haka bai kamata a ce za a dorawa wani alhakin iftila'in ba
  • Shugaban ya jajantawa gwamnati, al’ummar Maiduguri da ma jihar Yobe da duk jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa a fadin kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Shugaba Bola Tinubu ya ce ambaliyar da ta mamaye mafi yawan birnin Maiduguri mukaddari ce daga Allah da bai kamata a dora wa kowa laifi ba.

Shugaban ya yi wannan magana ne a ranar Litinin yayin wata ziyara da ya kai Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Kara karanta wannan

Ambaliyar Maiduguri: Ya na murna ya tsere daga kurkuku, jami'an tsaro sun cafke shi

Shugaba Tinubu ya yi magana kan abin da ya jawo ambaliya a Maiduguri
Tinubu ya jajantawa mutanen Maiduguri bayan ambaliya, ya ce ka da a zargi kowa. Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Tinubu ya kai ziyara gidan gwamnatin Borno da fadar Shehun Borno da kuma sansanin ‘yan gudun hijira (IDP) kamar yadda The Cable ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya yi magana kan ambaliya

Shugaban kasar ya ce bai kamata a dorawa wani laifin ambaliyar ba domin ita kanta gwamnatin ba ta da karfin ikon hana faruwar iftila'in.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ya ruwaito shugaban kasar yana cewa:

"Ambaliyar mukaddari ce daga Allah. Ba wani ne ya haifar da ita ba. Bai kamata mu fara zargin wani ba. Mu dai yi addu'a ga Allah ya jikan wadanda suka rasu."

Tinubu ya jinjinawa Zulum

Shugaban ya kuma ce yana ta yin tunani kan yadda za a magance irin wannan iftila'i da kuma matsalolin da sauyin yanayi ke haddasawa.

Kara karanta wannan

Ambaliyar Maiduguri: Shugaba Tinubu zai nema wa jama'a taimako, ya kafa asusun tallafi

“Na yi farin ciki da cewa Farfesa Zulum ya kasance jajirtaccen gwamna. Bari in tabbatar muku da cewa za mu kasance tare da jihar Borno kuma za mu dauki nauyin tare."

- A cewar Tinubu.

Shugaban ya jajantawa gwamnati, al’ummar jihar Yobe, da duk jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa, ya kuma yi alkawarin ci gaba da tallafawa wadanda bala’o’in ya shafa.

"Za a sake gina Maiduguri" - Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Tinubu ya sanar da cewa zai samar da gidauniyar bada agaji domin sake gina al’ummar Borno da ambaliyar ta shafa.

Ya ce idan aka dauki karamin kaso daga FAAC aka sanya shi a asusun ba da agajin, za a rage radadin da jama'a suke ciki tare da ba su tabbacin ana tare da su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.