'Yan Bindiga Sun Kara Kai Faramaki Filato, Matasa 5 Sun Kwanta Dama
- Wasu miyagun yan bindiga sun salwantar da rayukan matasa a Bokkos da ke jihar Filato biyar a daren Lahadi
- Lamarin ya afku a lokacin da matasan ke dawo wa kauyensu, inda su ka yi kicibis da yan bindigar da sojoji suka koro
- Mazauna yankin sun bayyana takaicin rashin samun taimakon jami'an tsaro har sai bayan yan ta'addan su ka gama barna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Plateau - Wasu mutane dauke da miyagun makamai sun farmaki mazauna Mbar a karamar hukumar Bokkos da ke jihar Filato.
Yan bindiga sun kai hari garin a daren Lahadi, inda su ka kashe mazauna yankin biyar, dukkaninsu matasa.
Channels Television ta wallafa cewa shugaban kuniyar ci gaban Bokkos, Farmasun Fuddanga ya tabbatar da harin, inda ya ce matasan ba su yi wa yan bindigar komai ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda yan bindiga su ka farmaki matasa
Shugaban ci gaban Bokkos, Farmasum Fuddang ya bayyana cewa wasu yan bindiga sun kai hari kan matasan a hanyar dawowa yankin daga Mbar a Filato.
Daily Post ta wallafa cewa shugaban ya bayyana cewa matasan ba su dauke da makamai a lokacin da yan bindiga su ka far masu bayan sojoji sun koro su daga wasu yankunan.
“Yan bindiga sun ci bulus:” Kungiyar Bokkos
Mista Farmasum Fuddanga ya bayyana takaicin yadda jami’an tsaro su ka gaza kawo masu agaji a kan lokaci har aka yi barna.
Shugaban kungiyar ya ce sai bayan yan bindigar sun kammala mugun aikinsu, sun kuma tafi kafin jami’an tsaro su karaso da zummar taimaka masu.
Sojoji sun kama dan bindiga a Filato
A wani labarin, kun ji yadda dakarun rundunar sojojin kasar nan su ka cafke wani fitinannen dan bindiga, Husseini Usman wanda ya hana jama'a zaman lafiya, musamman a jihar Filato.
Bayan an yi ram da dan ta'addan a kauyen Gawunari, karamar hukumar Riyom, Husseini Usman ya tabbatar da kai munanan hare-haren kan jama'ar da ba-su-ji-ba, ba-su-gani- ba.
Asali: Legit.ng