Hadarin Maulidi: Gwamnan Kaduna Ya Dimauta, Ya Daukarwa Dangi Alkawari

Hadarin Maulidi: Gwamnan Kaduna Ya Dimauta, Ya Daukarwa Dangi Alkawari

  • Gwamnatin Kaduna ta mika ta'aziyya ga iyalan mutum 40 da su ka rasu a hanyar Saminaka da ke kamarnar hukumar Lere a hadari
  • Mutanen sun rasu ne a hanyarsu ta zuwa maulidi, yayin da akalla mutum 48 da su ka tsira da rai, su ke asibiti su na karbar magani
  • Gwamnan jihar, Uba Sani ya bayyana alhini kan afkuwar hadarin, tare da mika jaje ga iyalan wanda su ka ji raunuka da ke asibiti

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Gwamnan Kaduna, Uba Sani ya mika ta’aziyya ga iyalan wadanda su ka rasu a hadarin mota da ya afku a Saminaka da ke karamar hukumar Lere.

Kara karanta wannan

An koma makoki bayan mutuwar ƴan Maulidi 36 a hatsarin mota, wasu 31 na asibiti

Gwamnan ya mika ta’aziyyarsa a wata sanarwa da ya fitar da kansa a ranar Litinin domin jajanta wa mazauna jihar da iftila'in hadari ya rutsa da su.

Kaduna
Gwamnan Kaduna ya yi ta'aziyya bayan mutuwar mutum 40 a hadarin mota Hoto: Uba Sani
Asali: Facebook

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa gwamnan ya shiga dimuwa da samun rahoton rasuwar mutanen da ke hanyarsu ta zuwa Maulidi a Saminaka da ke jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane 40 sun rasu a Kaduna

Mutane akalla 40 ne aka tabbatar da rasuwarsu a Kaduna yayin da su ke hanyar zuwa maulidin fiyayyen halitta, Annabi SAW a jihar Kaduna.

Zuwa yanzu, wasu mutum 48 na asibiti su na karbar magani a mummunan hadarin da ya ratsa zukatan jama’a.

Hadarin mota: Gwamnatin Kaduna za ta taimaka

Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya yi alkawarin cewa za su tallafa wa iyalan mutanen da hadari ya rutsa da su.

Kara karanta wannan

Jama'a sun razana bayan jami'ai da bindigu sun yi awon gaba da kantoma a Kano

Sanarwar da gwamnan ya fitar ta bayyana cewa za a taimaka masu domin rage radadin da su ke ciki a yanzu.

Yan maulidi sun rasu a Kaduna

A baya mun ruwaito cewa jama'a a Saminaka da ke Kaduna sun fuskanci wani mummunan al'amari biyo bayan hadarin mota da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 30.

Daga baya an samu karin rasuwar wasu, inda alkaluma su ka ce mutum 40 sun riga mu gidan gaskiya yayin da su ke hanyar zuwa Saminaka domin halartar maulidin Annabi SAW.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.