N950/lita: Yan Kasuwa Na Shirin Fara Shigo da Fetur saboda Tsadar Man Dangote

N950/lita: Yan Kasuwa Na Shirin Fara Shigo da Fetur saboda Tsadar Man Dangote

  • Masu kasuwancin mai sun bayyana cewa fetur din da matatar Dangote ta tace ya yi matukar tsada a kasuwa
  • Wannan ta sa yan kasuwar su ka fara sayo man fetur da kudinsu kai tsaye daga kasashen wajen zuwa kasar nan
  • Haka kuma sun bayyana rashin jin dadin yadda kamfanin NNPCL ya zama shi kadai ne ke dakon fetur daga matatar Dangote

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Yan kasuwar mai sun bayyana cewa dole su rika nema tare da shigo da man fetur daga kasashen waje.

Yan kasuwar na ganin wannan ya biyo bayan tsadar da farashin fetur da matatar Dangote ta samar bayan kamfanin NNPCL ya fitar da farashinsa a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Sabani ya kuma shiga tsakanin Dangote da NNPCL kan sabon farashin man fetur

Kamfanin
Yan kasuwa za su fara shigo da fetur daga ketare Hoto: Dangote Industries|NNPCL Limited
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa sun fara neman man fetur da za a kawo masu domin su fara sayar wa a gidajen man da ke kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan kasuwa na jiran isowar fetur

Masu dakon man fetur sun bayyana cewa fetur da su ka sayo daga kasashen waje zai fara shigo wa Najeriya a ranar Talata (yau).

Haka kuma sun nemi masu ruwa da tsaki su tabbatar da bayyana yadda aka fitar da farashin fetur da NNPCL ya dauko daga kamfanin Dangote.

Masu kasuwancin fetur sun fusata

Yan kasuwa masu zaman kansu sun bayyana takaicin yadda kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya zama shi kadai ke dakon fetur daga kamfanin Dangote.

Wata majiya daga kungiyar masu kasuwancin man fetur (IPMAN) ta bayyana cewa bai dace a ce NNPCL ne kawai mai dauko fetur domin sayar wa jama'a ba.

Kara karanta wannan

NNPCL ya fara dakon fetur daga matatar Dangote, an hango sauki ga 'yan Najeriya

An samu sabani tsakanin NNPCL da Dangote

A wani labarin kun ji cewa kamfanin mai na kasa (NNPCL) da matatar Dangote sun fitar da bayanai masu karo da juna kan yadda aka sayar da fetur ga kamfanin.

An samu sabanin ne bayan NNPCL ya ce ya sayi fetur da tsada a matatar Dangote, yayin da Dangote ya yi martani da cewa da Dala aka sayar wa NNPCL fetur ba Naira ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.