An Shiga Makoki bayan Mutuwar Ƴan Maulidi 36 a Hatsarin Mota, Wasu 31 na Asibiti

An Shiga Makoki bayan Mutuwar Ƴan Maulidi 36 a Hatsarin Mota, Wasu 31 na Asibiti

  • Mutane da dama masu bikin Maulidi sun rasa rayukansu bayan mummunan hatsarin mota a jihar Kaduna
  • Akalla mutane 36 aka tabbatar sun mutu inda da dama ke kwance a asibiti a hatsarin da ya faru a hanyar Saminaka
  • Masu bikin Maulidin sun shirya zuwa Saminaka ne daga Kwandare kafin haduwa da iftila'in a garin Lere

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Akalla mutane 36 aka tabbatar sun rasa rayukansu dalilin hatsarin mota a jihar Kaduna a kokarin zuwa Maulidi.

Lamarin ya faru ne a jiya Litinin 16 ga watan Satumbar 2024 a kokarinsu na zuwa Saminaka domin bikin Maulidi.

Mutane 36 sun mutu a hatsarin mota yayin zuwa bikin Maulidi
An rasa rayuka da dama a jihar Kaduna bayan hatsarin mota ana bikin Maulidi. Hoto: Legit.
Asali: Original

Mutanen Maulidi 36 sun mutu a hatsari

Kara karanta wannan

An yi mummunan haɗari a ranar Maulidi, mutane kusan 20 sun kone kurmus

The Guardian ta ruwaito cewa moar bas din ta ci karo da wata babbar motar tirela kusa da garin Lere da ke jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani ma'aikaci a hukumar ba da agajin gaggawa a jihar ya tabbatar da mutuwar mutane 36 a bangarensu, cewar rahoton Channels TV.

Wanda ya shirya bikin, Dayyabu Ahmad ya ce yanzu wadanda suka rasa rayukansu sun kai 40 yayin da 31 ke asibiti.

"Sun bar Kwandare domin zuwa Saminaka bayan sun iso Lere Allah ya kaddara suka ci karo da tirela."
"Binciken da muka yi ya tabbatar da cewa mutane 71 ne a cikin motar bas da ta yi hatsarin."

Ahmad Dayyabu

Hatsari ya ritsa da mutane 70

Har ila yau, wani da suka shirya bikin Maulidi mai suna Malam Abdullahi ya ce hatsarin ya rusa musu dukan shirin da suka yi.

Kara karanta wannan

Hadarin maulidi: Gwamnan Kaduna ya dimauta, ya daukarwa dangi lkawari

Abdullahi ya ce akwai wata motarsu da ta ci karo da mai babur inda wasu suka rasa rayukansu.

"Na kirga mutane 70 a cikin motar da suka hada da yara da mata, tabbas abin bakin ciki ne, mun dauki wasu zuwa asibitin koyarwa na JUTH da ke Jos."

- Mallam Abdullahi

Kano: An rasa rayuka a hatsarin mota

Kun ji cewa wani mummunan hatsarin mota da ya auku a jihar Kano ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutum tara har lahira.

Kakakin rundunar kiyaye haɗurra ta ƙasa reshen jihar Kano ya ce hatsarin ya auku ne tsakanin wata babbar mota da adaidaita sahu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.