'Yan Bindiga Sun Tashi Bama Bamai a Ofishin Ƴan Sanda, An Rasa Rayuka
- Ƴan bindiga sun kai hari tare da tashin bama-bamai a wani caji ofis na ƙaramar hukumar Orumba ta Kudu a jihar Anambra
- Rahotanni daga mazauna yankin sun nuna cewa maharan sun kashe ƴan sanda uku, wasu da dama sun samu raunuka
- Kakakin ƴan sandan Anambra, Tochukwu Ikenga ya ce jami'an tsaro sun kwance bama-bamai biyar a wurin bayan tafiyar maharan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Anambra - Wasu ƴan bindiga da ake kyautata zaton mayaƙan kungiyar IPOB ne sun kai mummunan hari caji ofis na ƴan sanda a jihar Anambra.
Bayanai sun nuna cewa ƴan ta'addan sun hallaka jami'an ƴan sanda uku a harin wanda suka yi amfani da bama-bamai yau Litinin, 16 ga watan Satumba, 2024.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:00 na safiyar ranar Litinin a karamar hukumar Orumba ta Kudu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami'an tsaro sun gano ƙarin bama-bamai
Bayan harin, jami’an tsaron hadin gwiwa da suka hada da sojoji, ƴan Sanda, jami'an NSCDC da ‘yan banga sun gano wasu bama-bamai guda biyar da ba su kai ga tashi ba a wurin.
Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigar na yunkurin tabbatar da bin dokar zaman gida ta ranar Litinin a lokacin da suka yi arangama da jami'an tsaro.
Ganau sun shaida cewa aƙalla ƴan sanda uku ne suka rasa rayukansu a harin, wasu kuma sun samu raunuka.
An kashe ƴan sanda a bakin aiki
A ruwayar Daily Trust, jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Anambra, Tochukwu Ikenga ya tabbatar da cewa jami'an ƴan sanda biyu aka kashe a harin.
"Maharan waɗanda ake zargin ƴan haramtacciyar ƙungiyar ƴan aware ne sun kutsa kai caji ofis ɗauke da bama-bamai, suka buɗe wuta kan mai uwa ɗa wani, wuta ta kama."
"Abin takaici ƴan sanda biyu da suka yi kokarin ɗaƙile harin sun rasa rayukansu, tuni aka ajiye gawarwakinsu a ɗakin ajiyar gawa," in ji Ikenga.
Ƴan bindiga sun shiga sakatariyar ƙaramar hukuma
A wani rahoton kuma wasu yan bindiga kimanin 30 sun dura ƙaramar hukumar Ogbaru a jihar Anambra inda suka bude wuta a sakatariya.
Rahotanni sun nuna cewa yan bindigar sun yi kone kone a karamar hukumar kafin su yi musayar wuta da yan sandan jihar.
Asali: Legit.ng