"Ku Taimaka Mana:" Gwamnan Katsina Ya Mika Bukatu ga Rundunar Sojan Sama
- Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya nemi karin tallafi daga rundunar sojan saman kasar nan wajen ragargazar yan ta'adda
- Dr. Dikko Radda ya bayyana cewa gwamnatinsa na bakin kokarinta wajen kakkabe rashin tsaro a fadin jihar, amma sai an kara kokari
- Ya shaida wa babban hafsan sojan saman kasar nan, Air Marshal Hassan Abubakar cewa akwai bukatar karin hadin kai tsakaninsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Katsina - Gwamnatin Katsina ta jaddada aniyarta na kakkabe rashin tsaro da ya addabi jam'ar da ke kauyuka da birnin jihar, tare da bunkasa noma.
Gwamna Dikko Umaru Radda ya tabbatar da haka a lokacin da ya karbi bakuncin babban hafsan sojin saman kasar nan, Air Mashal Hassan Abubakar a gidan gwamnatin Katsina.
Jaridar Punch ta wallafa cewa gwamna Radda ya roki rundunar sojojin saman ta rubinya kokarinta wajen taimaka wa Katsina a kawar da rashin tsaro.
Gwamna Radda ya daukar wa sojoji alkawari
Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya dauki alkawarin taimaka wa jami'an tsaron kasar nan da duk abin da su ke bukata wajen yakar rashin tsaro.
Radda ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, inda ya jaddada muhimmancin ci gaba da samun hadin kai da aiki tare tsakanin gwamnati da jami'an tsaro kan rashin tsaro.
"Za mu kawar da rashin tsaro:" Sojoji
Hafsan rundunar sojan sama, Air Mashal Hassan Abubakar ya tabbatar wa gwamnatin jihar Katsina cewa ana yaki da ta'addanci a jihar.
Hafsan tsaron ya bayyana cewa ana kokarin kara jami'an tsaro a yankunan Daura da Funtua domin kara tsaurara tsaro.
Rashin Tsaro: Gwamna Radda zai dauki mataki
A wani labarin kun ji cewa gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda ya fara daukar matakan yakar yan ta'adda da su ka addabi jihar, inda za a hada kai da mutanen gari ta hanyar ba su bindigu.
Gwamnan zai dauki matakin ne saboda karancin jami'an tsaro, inda ya shawarci dukkanin masu sha'awar kare kauyukansu da su mika bayanan su ga gwamnatin jihar domin a tantance su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng