Sabani Ya Kuma Shiga Tsakanin Dangote da NNPCL kan Sabon Farashin Man Fetur

Sabani Ya Kuma Shiga Tsakanin Dangote da NNPCL kan Sabon Farashin Man Fetur

  • A yayin da yan Najeriya ke cigaba da tsammanin sauki a kan farashin fetur an samu sabani tsakanin NNPCL da matatar Dangote
  • An samu bayanai mabanbanta kan yadda cinikin man fetur ya kullu tsakaninsu inda suka fitar da sanarwa mai karo da juna
  • A daya bangaren, yan kasuwa sun koka kan cewa har yanzu ba su samu bayani a hukumance daga NNPCL kan farashin man ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ana cigaba da samun sabani tsakanin matatar Dangote da kamfanin NNPCL a kan farashin man fetur.

Kamfanin NNPCL ya bayyana cewa ya saye litar man fetur a N898 sai kuma Dangote ya ce ba a Naira suka yi ciniki ba.

Kara karanta wannan

NNPCL ya fara dakon fetur daga matatar Dangote, an hango sauki ga 'yan Najeriya

Matatar Dangote
An samu sabanin farashin mai tsakanin Dangote da NNPCL. Hoto: Dangote Industries|NNPCL Limited
Asali: UGC

Jaridar Punch ta wallafa cewa kungiyar yan kasuwa ta bayyana cewa har yanzu ba ta samu bayani kan farashin man fetur daga NNPCL ba.

Maganar NNPCL kan farashin man Dangote

An samu rahotanni kan cewa kamfanin NNPCL ya saye litar man fetur a matatar Dangote a kan N898.

Haka zalika NNPCL ya ce ya dauko mai lita miliyan 16.8 ne maimakon lita miliyan 25 da matatar Dangote ta sanar a farko.

Matatar Dangote ta yi maratani ga NNPCL

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa matatar Dangote ta musa maganar cinikin man fetur da Naira da kamfanin NNPCL ya fada.

Matatar Dangote ta ce babu ƙamshin gaskiya a cikin lamarin kuma sai a watan Oktoba ne za su fara cikin man fetur da Naira.

Yan kasuwa na jiran farashin man fetur

Kara karanta wannan

N857 zuwa N865/Lita: An hango farashin da Dangote zai sayar da fetur a Najeriya

Kungiyar yan kasuwar man fetur ta ce har yanzu ba ta samu bayani a hukumance kan sabon farashin man fetur daga NNPCL ba.

Shugaban kungiyar IPMAN, Abubakar Maigandi ya ce kawai sun ga sanarwa ne a kan farashin man fetur din ba tare da samun takarda daga NNPCL ba.

SERAP ta maka Tinubu a kotu

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar kare hakkokin tattalin arziki (SERAP) ta maka Shugaba Bola Tinubu a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Kungiyar SERAP ta shigar da Tinubu da ministan shari'a, Mista Lateef Fagbemi da kuma NNPCL kara kan karin kudin man fetur a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng