Rai Ya Ɓaci: Matasa Sun Babbaka Yan Bindiga a Arewacin Najeriya
- Rahotanni da suke fitowa daga jihar Kaduna na nuni da cewa masu matasa sun cinna wuta kan gawar wasu da ake zargi yan bindiga ne
- An ruwaito cewa lamarin ya faru ne a kauyen Nasarawa-Azzara a karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna a Arewacin Najeriya
- Hakan na zuwa ne bayan sojojin Najeriya sun yi nasarar kai farmaki kan wasu yan ta'adda a yankin tare da kashe da dama cikinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Wasu matasa a jihar Kaduna sun nuna bacin rai kan gawarwakin wasu da ake zargi yan bindiga ne.
An ruwaito cewa matasan sun banka wuta kan yan bindigar ne yayin da suka samu gawarsu a jeji.
Aminiya ta wallafa cewa lamarin ya faru ne a garin Nasarawa-Azzara a karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun hallaka yan bindiga a Kaduna
A ranar Laraba da ta gabata ne sojojin Najeriya suka kai farmaki kan yan ta'adda a ƙauyen Nasarawa-Azzara.
A yayin harin, an ruwaito cewa sojojin Najeriya sun yi nasarar hallaka wasu miyagun yan bindiga guda uku.
Matasa sun banka wuta ga yan bindiga
A ranar Lahadi aka samu labarin cewa mutanen garin Nasarawa-Azzara suka samu gawar da ake tunanin ta yan bindigar da sojojin suka kashe ne.
Biyo bayan haka kuma cikin gaggawa suka cinna wuta ga gawarwakin a Hayin Dam da ke kusa da garinsu.
Maganar dan banga kan kona yan bindiga
Wani dan banga a garin Nasarawa-Azzara mai suna Hassan ya ce matasan su kona yan bindigar ne kafin zuwansu.
Manema labarai sun yi kokarin jin ta bakin kakin yan sanda a jihar Kaduna amma hakan bai samu ba har a wannan lokacin.
Soja ya harbe matashi har lahira
A wani rahoton, kun ji cewa rahotanni da suka fito daga jihar Benue na nuna an samu yamutsi bayan an zargi wani sojan Najeriya da harbe wani mutum.
An ruwaito cewa matasa sun nuna bacin rai yayin da suka so tayar da rikici bayan an dauki gawar mutumin da sojan ya bindige har lahira.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng