Labarin Husaina: Hedikwata Ta Yi Magana kan Zargin Janar da Zalunci, An Dauki Mataki
- Hukumar tsaron kasar nan (DHQ) ta magantu kan bidiyon wata mata, Hussaina Ilyasu da ke zargin an tsare mijinta ba bisa ka'ida ba
- Labarin Hussaina ya karade kafafen sada zumunta inda ta ce wani jami'in sojan ruwa MS Adamu da cin zarafin mijinta, Seaman Abbas Haruna
- A sanarwar da DHQ ta fitar, ta dauki alkawarin gudanar da bincike da zummar tabbatar da adalci a zargin tsare sojan har na shekara shida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Hukumar tsaron kasar nan (DHQ) ta bayyana cewa labarin wata matar sojan ruwa, Hussaina Ilyasu ya zo mata na zargin yi wa mijinta rashin adalci.
Labarin Malama Hussaina Ilyasu ya dauki hankali bayan ta zargi wani babban jami'in sojan ruwa, MS Adamu da tsare mijinta, Seaman Abbas Haruna har ya haukace.
A sakon da jami'in labaran hukumar tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau ya fitar, kuma tsohon hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya wallafa, ya ce Hedikwata za ta dauki mataki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a binciki batun MS Adamu da Seaman Haruna
Jaridar Aminiya ta tattaro cewa karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya ce an fara bincike kan zargin tsare Seaman Haruna ba bisa ka'ida.
Wannan na kunshe a sanarwar da mai magana da yawun karamin Ministan, Ahmed DanWudil ya fitar, inda ya ce binciken ya zama tilas domin a yi adalci.
Wane zargi ake yi wa Janar MS Adamu?
Malama Hussaina ta bayyana a shirin Berekete TV inda cikin hawaye ta bayyana cewa an jawo mijinta, Seaman Abbas Haruna ya rasa hankalinsa.
Ta zargi kwamandansa, MS Adamu da bayar da umarnin a tsare Seaman Haruna tare da azabtar da shi saboda ya je sallar Juma'a ba tare da izini ba.
Yaron shugaban DSS ya saci kudi?
A baya mun ruwaito cewa Abba Bichi, dan tsohon shugaban hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), Yusuf Magaji Bichi ya musanta zargin cewa ya sace kudin mahaifinsa.
Abba Bichi ya bayyana cewa ana yada labarin ne mara tushe domin ana son a bata masa suna, amma babu gaskiya a zancen ya sace kudin mahaifinsa Dala Miliyan biyu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng