Kamfanin NNPCL Ya Bayyana Farashin da Zai Sayar da Fetur Na Matatar Dangote
- Kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ya bayyana farashin da zai sayar da man fetur da ya dauko daga matatar Dangote
- A jihohin yankin Arewa maso Gabas farashin man fetur a gidajen mai mallakin NNPCL zai kai N1,019 kan kowace lita
- A jihohin Kudancin Najeriya irin su Rivers da Oyo farashin da NNPCL zai sayar da fetur ɗin ya kai N960 kan kowace lita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ya fitar da jadawalin yadda farashin man fetur na matatar Dangote zai kasance a jihohin Najeriya.
Kamfanin NNPCL ya bayyana cewa zai sayar da man fetur da aka ɗauko daga matatar Dangote a kan farashin sama da N1,000 kan kowace lita a yankin Arewa maso Gabas.
Mai magana da yawun kamfanin NNPCL, Olufemi Soneye, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa ta shafin X na kamfanin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NNPCL ya bayyana farashin sayar da fetur
Oluyemi Soneye ya bayyana cewa farashin zai iya kai wa N1,019 kan kowace lita a wurare kamar jihar Borno da kuma N999.22 a Abuja, Sokoto, Kano da sauransu.
A jihohin Oyo, Rivers da sauran yankunan Kudu, zai kasance kan N960 a kowace lita.
Farashi mafi ƙaranci wanda da kamfanin NNPC ya fitar, shi ne na N950 a Legas da kewaye.
"Kamfanin NNPCL ya fitar da ƙiyasin farashin man fetur (wanda aka samu daga matatar Dangote) a tashoshin kamfanin da ke a faɗin ƙasar nan."
"Kamfanin NNPCL yana so ya bayyana cewa, bisa ga tanade-tanaden dokar masana’antar mai, farashin fetur ba gwamnati ta ƙayyade ba, amma ana tattaunawa kai tsaye tsakanin ɓangarorin"
- Oluyemi Soneye
Ya ƙara da cewa kamfanin NNPCL ya siyo fetur ɗin ne da Dala a hannun Dangote yayin da zai fara saya da Naira a ranar 1 ga watan Oktoban 2024.
NNPCL ya fara dakon fetur daga matatar Dangote
A wani labarin kuma, kun ji cewa ranar Asabar, 14 ga watan Satumba, kamfanin NNPCL ya sanar da cewa ya fara girke motocinsa a harabar matatar man Dangote domin fara jigilar fetur.
A ranar Lahadi, 15 ga watan Satumban 2024 motocin kamfanin NNPCL suka fara lodi da dakon man fetur daga matatar Dangote wacce ke a jihar Legas.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng