Bichi: Ɗan Tsohon Daraktan DSS Ya Yi Martani kan Zargin Sace $2m na Mahaifinsa
- Yayin da ake ta yada cewa Abba Bichi ya tsere da kudin mahaifinsa, matashin ya yi martani kan rade-radin da ake yi
- Abba wanda ɗa ne ga tsohon daraktan DSS, Yusuf Magaji Bichi ya ƙaryata jita-jitar inda ya ce ana son bata musu suna ne
- Wannan na zuwa ne bayan rade-radin cewa Abba ya sace kudin mahaifinsa har $2m inda ake zargin ya tsere da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Dan tsohon daraktan DSS, Yusuf Magaji Bichi ya yi martani kan rade-radin da ake yi a kansa
Abba Bichi ya musanta labarin cewa ya tsere bayan sace $2m na mahaifinsa da ake ta yadawa a kafofin sadarwa.
Abba Bichi ya ƙaryata jita-jitar satar $2m
Matashin dan kwallon ya ce babu kamshin gaskiya a labarin inda ya ce an yi ne domin bata musu suna, cewar rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abba ya yi martanin ne yayin da ya ke cikin wani filin wasa a kasar Jamus inda ya ce ya mayar da hankalinsa kan wasan kwallon kafa.
"Ba gudu na ke yi ba, ina faman gina rayuwa ta ne a matsayin dan kwallo, jita-jitar da ake yadawa karairayi ne kuma abin dariya."
- Abba Bichi
Yusuf Bichi ya yi fatali da rade-radin
Har ila yau, Yusuf Bichi shi ma ya yi magana kan lamarin inda ya yi fatali da rade-radin da ake yadawa.
Yusuf Bichi ya nuna goyon baya ga dan nasa musamman bayan ƙungiyarsa ta yi rashin nasara a wasan da ta buga, cewar rahoton Pulse.
DSS ta cafke lakcara a Jami'ar Abuja
Kun ji cewa ana zargin jami'an hukumar DSS a Najeriya sun kama wani lakcara a Jami'ar Baze da ke birnin Abuja, Dr. Abubakar Alkali.
An wuce da Alkali ne zuwa jihar Sokoto fiye da makwanni uku kan zargin goyon bayan zanga-zanga da aka yi a Najeriya.
Wannan na zuwa ne bayan gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024.
Asali: Legit.ng