NNPCL Ya Fara Dakon Fetur daga Matatar Dangote, An Hango Sauki ga 'Yan Najeriya

NNPCL Ya Fara Dakon Fetur daga Matatar Dangote, An Hango Sauki ga 'Yan Najeriya

  • Rahotanni sun bayyana cewa motocin kamfanin NNPCL sun fara lodi da dakon man fetur daga matatar man Dangote da ke Lekki, jihar Legas
  • An ce tun a ranar Asabar NNPCL ya girke motocinsa a harabar matatar inda kuma a yau Lahadi Dangote ya fara lodawa motocin feturinsa
  • Mataimakin shugaban kamfanin Dangote, Devakumar V.G. Edwin ya ce matatar Dangote na da karfin fitar da lita miliyan 54 a kowacce rana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - A ranar Asabar kamfanin NNPCL ya sanar da cewa ya fara girke motocinsa a harabar matatar man Dangote da ke Ibeju, Lekki domin fara jigilar fetur.

Da misalin karfe 2:00 na yau Lahadi aka rahoto cewa motocin kamfanin NNPCL sun fara lodi da dakon man fetur daga matatar Dangote.

Kara karanta wannan

Daga karshe gwamnatin tarayya ta fadi lokacin fara jigilar fetur daga matatar Dangote

Kamfanin NNPCL ya fara lodi da dakon man matatar Dangote a ranar Lahadi
Dangote ya ce matatarsa za ta iya fitar da litar fetur miliyan 54 yayin da NNPCL ya fara jigilar man. Hoto: @nnpclimited
Asali: Twitter

NNPCL ya fara jigilar man Dangote

Rahoton NTA ya nuna cewa motocin NNPCL 10 ne suka tsaya kan famfunan zuba man yayin da aka cika tankunansu da fetur ta hanyar amfani da wata na'urar zamani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce matatar Dangote na da famfunan zuba mai guda 86 wanda ke nufin za a iya zubawa motoci 86 mai a lokaci daya.

Ana ganin wannan tsarin zai taimakawa kamfanin NNPCL a kokarinsa na ganin man fetur ya wadata a fadin kasar nan, kasancewar famfuna 40 fetur kadai suke zubawa.

Dangote ya kawo sauki ga Najeriya

Mataimakin shugaban kamfanin Dangote, Devakumar V.G. Edwin ya ce matatar Dangote na da karfin fitar da lita miliyan 54 a kowacce rana.

A cewar Devakumar V.G. Edwin, wannan zai kare kasar Najeriya daga barazanar sauyi a musayar kudin kasashen waje.

Kara karanta wannan

'Yan kasuwa sun gama karaya da matatar Dangote, sun fadi sharadin sayen fetur

Kalli bidiyon motocin farko da suka fara jigilar man Dangote:

Farashin fetur na iya sauka

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan Najeriya sun fara samun kwanciyar hankali bayan da bayanai suka nuna cewa farashin fetur na iya saukowa zuwa kasa da N865.

An ta tattaro cewa akwai yiwuwar kamfanin NNPCzai sayi fetur daga matatar Dangote a kan N960/N980 kan kowace lita yayin da zai sayar wa ‘yan kasuwa a kan N840/N850.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.