Sokoto: Mummunar Gobara Ta Babbake Ofisoshi 6 a Hedikwatar 'Yan Sandan Najeriya

Sokoto: Mummunar Gobara Ta Babbake Ofisoshi 6 a Hedikwatar 'Yan Sandan Najeriya

  • Gobara ta kone ofisoshi shida da ke cikin sashin gudanarwa na hedikwatar 'yan sandan jihar Sokoto yayin da wutar ta tashi a ranar Asabar
  • Har yanzu ba a san musababbin tashin gobarar ba amma daukar matakin gaggawa da jami’an kashe gobara suka yi ya dakile karin barna
  • Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta lalata ofisoshin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, dakin bauta da ofishin babban limamin rundunar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sokoto - Rahotanni sun bayyana cewa wata mummunar gobara ta tashi a hedikwatar rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Sokoto.

Gobarar wadda ba a iya tantance musabbabinta ba, a safiyar ranar Asabar ta kone ofisoshi shida a hedikwatar rundunar ‘yan sandan.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana tallafin da za ta kaiwa mutanen Maiduguri

Rundunar 'yan sanda ta yi magana kan gobarar da ta tashi a hedikwatarta da ke Sokoto
Gobara ta tashi a hedikwatar 'yan sandan jihar Sokoto. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Gobara ta kone hedikwatar 'yan sanda

Gobarar ta yi barna a bangaren gudanarwar hedikwatar kafin jami'an kashe gobara su shawo kan ta inji rahoton The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce gobarar ta tashi da misalin karfe 5 na safiya kuma ta lalata ofisoshin mataimakin kwamishina mai kula da harkokin mulki, dakin bauta da ofishin babban limamin rundunar.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Ahmed Rufa’i, ya ce gobarar ta lalata bangaren gudanarwa na hedikwatar.

Barnar da gobarar ta yi

Jaridar Daily Trust ta ruwaito ASP Ahmed Rufa’i na cewa:

“Kwarai, an samu tashin gobara a ranar Asabar a hedikwatar rundunar da ke jihar. “Lamarin ya shafi ofisoshi kusan shida da ke a bangaren gudanarwa.
“Gobarar ta kone wasu ofisoshi da suka hada da: Ofishin mataimakin kwamishina bangaren gudanarwa; ofishin sirri da na babban limamin rundunar.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS da ƴan sanda sun mamaye fadar Sarki bayan fara raɗe raɗin ya rasu

“Gobarar ta kuma lalata mana dakin bauta da kuma ofishin babban sufeto bangaren gudanarwa da kuma sauran kayayyaki amma babu rauni ko asarar rai.”

Sai dai Rufa’i ya ce babu wata makarkashiya a tashin gobarar, inda ya ce babu kowa a sashen lokacin da lamarin ya faru.

Gobara a ofishin 'yan sandan Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa a watan Fabrairun 2024, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayar da rahoton cewa gobara ta babbake ofishinta da ke karamar hukumar Nasarawa.

Kwamishinan 'yan sandan Kano (na wancan lokaci), Mista Usaini Gumel ya sanar da hakan yana mai cewa an fara tantance takardun da gobarar ta lalata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.