'Yan Bindiga Sun Hallaka Shugaban Babbar Kasuwa a Cikin Dare
- Ƴan bindiga sun yi ta'asa a jihar Enugu a wani harin da suka kai a ƙaramar hukumar Enugu ta Kudu
- Miyagun ƴan bindigan sun hallaka shugaban ƙungiyar ƴan kasuwar Ogbete bayan sun binidige shi har lahira
- Ƴan bindigan sun hallaka Stephen Aniagu ne a ranar Asabar bayan sun bi sahunsa lokacin da yake kan hanyar komawa gida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Enugu - Wasu ƴan bindiga sun kashe shugaban ƙungiyar ƴan kasuwar Ogbete a jihar Enugu da ke yankin Kudu maso gabashin Najeriya.
Kasuwar Ogbete ita ce babbar kasuwa a birnin Enugu babban birnin jihar Enugu.
Yadda ƴan bindiga suka kai harin
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa ƴan bindigan sun kashe Stephen Aniagu ne da misalin ƙarfe 7:00 na daren ranar Asabar.
Majiyoyi sun bayyana cewa an kai wa shugaban kasuwar harin ne a mahaɗar Moses Ogbodo da ke kusa da kasuwar Topland a yankin Amaechi Axis cikin ƙaramar hukumar Enugu ta Kudu.
Majiyoyin sun an kashe shi ne lokacin da yake kan hanyar komawa gida ne, bayan ƴan bindigan sun biyo sahunsa sannan suka harbe shi har lahira.
A wani faifan bidiyo da aka yaɗa, an nuna gawar marigayin kwance a cikin jini.
A cikin bidiyon an ji wasu mazauna yankin da suka taru a kusa da wurin suna yin Allah wadai kan kisan da aka yi masa.
Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?
Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Enugu, DSP Daniel Ndukwe, domin samun ƙarin bayani kan lamarin.
Kakakin ya bayyana cewa yana cikin Coci a lokacin amma a tura masa saƙo ta wayarsa.
"Yanzu haka ina cikin Coci ka tura min saƙo ne"
- DSP Daniel Ndukwe
Sai dai, har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ba.
Ƴan bindiga sun kashe sojoji
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari kan ma'aikatan kamfanin gine-gine a hanyar Funtua zuwa Gusau a jihar Zamfara.
Ƴan bindigan a yayin harin sun kashe mutane bakwai ciki har da sojoji uku waɗanda suke yi wa injiniyoyi ƴan ƙasashen waje rakiya.
Asali: Legit.ng