N857 zuwa N865/Lita: An Hango Farashin da Dangote Zai Sayar da Fetur a Najeriya

N857 zuwa N865/Lita: An Hango Farashin da Dangote Zai Sayar da Fetur a Najeriya

  • Rahotanni sun bayyana cewa akwai yiwuwar farashin fetur na iya saukowa zuwa N857 da N865 kan kowace lita a fadin kasar nan
  • Majiya mai tushe ta ce sabon tsarin da aka yi daga tattaunawar NNPC da Dangote zai baiwa ‘yan Najeriya damar samun fetur da araha
  • An tattaro cewa Dangote zai sayarwa NNPC litar fetur a kan N960/N980 yayin da zai kamfanin zai sayar wa ‘yan kasuwa a kan N840/N850

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - A jiya Asabar ne 'yan Najeriya suka fara samun kwanciyar hankali bayan da bayanai suka nuna cewa farashin fetur na iya saukowa zuwa N857 da N865 kan kowace lita.

Wannan bayanin na zuwa ne bayan da kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya fara jigilar man daga matatar Dangote a yau Lahadi.

Kara karanta wannan

Tsadar fetur: Fasinjoji a Kaduna sun hakura da hawa mota, sun nemawa kansu mafita

MAjiya mai tushe ta yi hasashen karyewar fetur bayan fara jigilar man Dangote
Ana hasashen litar fetur za ta sauka zuwa kasa da N850 bayan fara jigilar man Dangote. Hoto: Dangote Foundation
Asali: Facebook

Da yiwuwar farashin fetur ya sauko

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa NNPC da zai sayi fetur daga Dangote ne a kan N960/N980 kan kowace lita yayin da zai sayar wa ‘yan kasuwa a kan N840/N850.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan har wannan bayanin ya tabbata, to hakan zai sa 'yan kasuwa su sayar da fetur din a tsakanin N857 zuwa N865 kan kowace lita.

Sai dai kuma babu wani bayani kan ko farashin fetur din zai zama daya a dukkanin gidajen man kasar ko kuma kowanne gidan mai zai sanya farashinsa.

Farashin man fetur a halin yanzu

Ya zuwa jiya dai ana sayar da litar fetur a kan N855 a gidajen man NNPC da ke Legas kuma shi ne mafi arha yayin da manyan dillalan man ke sayar da shi kusan N920.

A gidajen ‘yan kasuwa masu zaman kansu, farashin ya haura N1,000. A wasu gidajen man kuma a fadin kasar, ana sayar da litar fetur a kan N1,200 ko sama da hakan.

Kara karanta wannan

'Yan kasuwa sun gama karaya da matatar Dangote, sun fadi sharadin sayen fetur

Majiya mai tushe ta ce sabon tsarin da aka yi daga tattaunawar NNPC da Dangote zai baiwa ‘yan Najeriya damar samun man fetur a tsakanin N857 zuwa N865 kowace lita.

NNPCL ya faɗi farashin man Dangote

A wani labarin, mun ruwaito cewa kamfanin man Najeriya (NNPCL) ya bayyana cewa yanayin kasuwa ne zai kayyade farashin man feturin Dangote.

Dangane da batun fara jigilar mai daga matatar Dangote, kamfanin NNPCL ya ce zai fara jigilar man da zarar wa'adin da matatar ta bayar na ranar 15 ga Satumbar 2024 ya cika.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.