Yadda Sojoji Suka Hallaka Wasu daga Cikin 'Yan Bindigan da Suka Kashe Sarkin Gobir

Yadda Sojoji Suka Hallaka Wasu daga Cikin 'Yan Bindigan da Suka Kashe Sarkin Gobir

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka wasu daga cikin ƴan bindigan da suka kashe Sarkin Gobir
  • Uku daga cikin ƴan bindigan da sojojin suka hallaka a jihar Zamfara na daga cikin waɗanda ke da hannu a kisan da aka yiwa marigayi Isah Mohammed Bawa
  • Ƙanin marigayi ya bayyana cewa majiyoyi sun tabbatar masa da cewa Halilu Sububu ne ya shirya sace marigayin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Dakarun sojoji sun hallaka wasu daga cikin ƴan bindigan da suka kashe Sarkin Gobir, marigayi Isa Mohammed Bawa.

Ƴan bindigan su uku na daga cikin waɗanda sojoji suka hallaka kwanan nan a wani artabu a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Ana jimamin ambaliyar ruwa, gini ya rufto kan daliban jami'a

Sojoji sun hallaka 'yan bindigan da suka kashe Sarkin Gobir
Wasu daga cikin 'yan bindigan da suka kashe Sarkin Gobir sun gamu da ajalinsu Hoto: Abbakar Ali
Asali: Facebook

Sanata Shu’aibu Gwanda Gobir, ƙanin marigayi sarkin ne ya tabbatar da hakan a zantawarsa da wakilin jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun kashe makasan Sarkin Gobir

Sanata Gobir ya ce waɗanda aka gano sun haɗa da Kachalla Buzu wanda aka fi sani da Halilu Sububu, Blacky da wani ɗan bindiga ɗaya, waɗanda suka fito a wani faifan bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta.

"Na tabbatar da hakan daga majiyoyi daban-daban. Halilu Sububu ne ya shirya sace marigayi sarki. Alhamdulillah yanzu sun girbi abin da suka shuka a hannun sojojin Najeriya."
"Insha Allah duk waɗanda ke da hannu wajen kashe Sarkin Gobir za su tarar da ƙarshensu a nan kusa ko a nan gaba. Jinin marigayi sarki ba zai tafi a banza ba saboda makasan shi sai sun girbi abin da suka shuka."

Kara karanta wannan

Halilu Sububu: Tinubu ya yabawa sojoji kan kisan shugaban 'yan bindiga

"Roƙo na ga gwamnatin tarayya shi ne dukkanin wayoyin da aka ƙwato daga hannun ƴan bindigan a bincike su sosai ta yadda gwamnati za ta gano mutanen da ƴan bindigan suke magana da su."

- Sanata Shuaibu Gwanda Gobir

Sanata Gobir ya ba da tabbacin cewa iyalan marigayi sarkin ba za su taɓa yin ƙasa a gwiwa ba a ƙoƙarinsu na ganin duk waɗanda ke da hannu a kisan an cafke su ko sojoji su hallaka su.

Sarakuna sun magantu kan kisan Sarkin Gobir

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar sarakunan gargajiya ta Kudancin Najeriya ta yi Allah-wadai kan kisan da ƴan bindiga suka yi wa Sarkin Gobir, marigayi Alhaji Isah Mohammed Bawa.

Majalisar ta kuma yi Allah wadai da yawaitar kashe-kashe da sace-sace da ake fama da su a ƙasar nan, inda ta buƙaci gwamnati ta tashi tsaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng