Rundunar Sojoji ta Gwangwaje Dakarun da Suka Hallaka Dan Ta'adda, Halilu Sabubu
- Rundunar sojojin Nigeriya ta ware makudan kudi domin ba dakarun da suka yi nasarar hallaka Halilu Sabubu
- Hafsan tsaron kasar, Janar Christopher Musa shi ya tabbatar da haka inda ya yabawa jami'an tsaron tare da kara musu karfin guiwa
- Wannan na zuwa ne bayan kisan rikakken dan ta'adda, Halilu Sabubu da aka yi a jiya Juma'a 13 ga watan Satumbar 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Zamfara - Rundunar sojoji ta yabawa dakarun da suka yi nasarar hallaka kasurgumin dan ta'adda, Halilu Sabubu.
Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya yi alkawarin kudi ga sojojin da suka hallaka san ta'addan.
Halilu Sabubu: An ba sojoji kyautar kudi
A cikin wani faifan bidiyo da @jrnaib2 ya wallafa a shafin X, an gano Janar Musa na yabawa dakarun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Janar Musa ya ce za a ba su makudan kudi har N1m ga sojojin da suka jagoranci kisan rikakken dan ta'addan da ya addabi al'umma.
Hafsan ya yabawa sojojin tare da yi musu godiya na musamman kan irin jajircewa da suka yi.
Yadda aka hallaka dan ta'adda, Halilu Sabubu
Wannan na zuwa ne bayan sojojin Najeriya sun yi nasarar hallaka rikakken dan ta'adda, Halilu Sabubu.
An yi ajalin Sabubu ne da wasu yan ta'adda da safiyar Juma'a 13 ga watan Satumbar 2024 a jihar Zamfara.
Kisan Halilu ya saka al'ummar Najeriya da dama farin ciki da suke ganin an dauko hanyar karya lagon miyagun.
Bidiyon Halilu Sabubu ba karshe kafin ajalinsa
A wani labarin irin wannan, mun kawo muku bidiyon da Halilu Sabubu ya fitar kwanaki uku kafin sojoji su hallaka shi a jihar Zamfara.
Sabubu ya fitar da bidiyo ne a ranar Talata 10 ga watan Satumbar 2024 inda yake neman alfarma daga sauran yan ta'adda kan kashe-kashe da ake yi.
A bidiyon, Sabubu ya bukaci takaita hare-hare da satar shanun Fulani inda ya bukaci su mayar da hankali kan jami'an tsaro kawai.
Asali: Legit.ng