Halilu Sububu: Tinubu Ya Yabawa Sojoji kan Kisan Shugaban 'Yan Bindiga
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna farin cikinsa kan nasarar da dakarun sojoji suka samu kan ƴan bindiga a yankin Arewa maso Yamma
- Shugaba Tinubu ya yabawa sojojin bisa nasarar da sojojin suka samu kan kisan shugaban ƴan bindiga, Halilu Sububu
- Shugaban ƙasan ya ba jami'an tsaro tabbacin ci gaba da ba su goyon baya a ƙoƙarin da suke yi na samar da tsaro a ƙasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan kisan da dakarun sojoji suka yiwa shugaban ƴan bindiga, Halilu Sububu.
Shugaba Tinubu ya yi farin ciki bisa nasararorin da sojoji suka samu kan ƴan bindiga a yankin Arewa maso Yamma.
Tashar Channels tv ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin Tinubu kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Asabar.
A cikin sanarwar ya bayyana cewa nasarorin da aka samu sun nuna cewa jami'an tsaron ƙasar nan a shirye suke wajen tabbatar da zaman lafiya da samar da tsaro.
Sojoji sun hallaka Halilu Sububu
Dakarun sojoji na Operation Hadarin Daji, a ranar Alhamis suka hallaka ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga, Halilu Sububu, wanda ya daɗe yana addabar mutanen Zamfara, Sokoto, da wasu jihohin Arewa maso Yamma.
Dakarun sojojin sun kuma hallaka wani ɗan ta'adda mai suna Sani Wala Burki tare da tarwatsa wata maɓoyar ƴan ta'adda a Kaduna inda suka kuɓutar da ɗalibai 13.
Me Tinubu ya ce kan kisan Halili Sububu
"Shugaba Tinubu ya yabawa rundunar sojoji, hukumomin leƙen asiri da dakarun sojoji bisa ƙoƙarinsu da jajircewarsu waɗanda suka sanya aka samu waɗannan nasarorin."
"Shugaba Tinubu ya kuma yabawa gaba ɗaya hukumomin tsaro bisa ƙarin tsaron da aka samu a ƙasa sannan ya buƙace su da su ƙara zage damtse har sai an kawar da duk wata barazanar tsaro."
"Shugaba Tinubu ya ƙara ba da tabbaci ga hukumomin tsaro na ci gaba da ba su goyon baya wajen cimma muradin samar da tsaro a ƙasar nan."
- Bayo Onanuga
Bidiyon Halilu Sububu na ƙarshe
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga, Halilu Sububu ya fitar da bidiyo ana saura ƴan kwanaki kaɗan sojoji su hallaka shi.
A cikin bidiyon an nuna yadda ƙasurgumin dan ta'addan ke roƙon Fulani yan uwansa kan kashe-kashen da ake yi a yankin Arewacin Najeriya.
Asali: Legit.ng