Mawaki Musulmi Ya Ayyana Kansa Fasto, Ya Fadi Wahayi da Ya Samu kan Marin Fasto

Mawaki Musulmi Ya Ayyana Kansa Fasto, Ya Fadi Wahayi da Ya Samu kan Marin Fasto

  • Mawaki Habeeb Okikiola Badmus ya bayyana dalilinsa na zabgawa Fasto mari a makon jiya a jihar Lagos da ake ta cece-kuce
  • Mawakin da aka fi kira da Portable ya ce shi ma Fasto ne kuma yana karbar wahayi daga sama domin ceto al'umma
  • Ya ce ya mari Faston ne saboda wahayin da ya samu daga sama domin gwada shi ko na gaskiya ne ko kuma jabu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Mawaki Habeeb Okikiola Badmus ya yi martani bayan zabgawa Fasto mari a jihar Lagos.

Mawakin da aka fi sani da Portable ya ayyana kansa a matsayin Fasto mai fadakarwa ga al'umma domin cetonsu.

Kara karanta wannan

"Ba zan sake mara maka baya a siyasa ba": Ministan Tinubu ga yaronsa gwamnan PDP

Mawaki Musulmi ya fadi dalilin zabgawa Fasto mari
Mawaki, Portable ya bayyana kansa a matsayin Fasto bayan marin malamin addini. Hoto: @portablebaeby.
Asali: Instagram

Lagos: Mawaki Portable ya ayyana kansa Fasto

Portable ya bayyana haka a shafinsa na Instagram inda ya fayyace komai game da marin Fasto da ya yi a Lagos.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mawakin ya ce shi ma Fasto ne wanda ya ke samun wahayi tare da fadakar da al'umma ayoyin Ubangiji.

Duk da yadda ake masa kallokaman shugaban yan daba a cikin al'umma, Portable ya ce shi bawan Allah ne na gaskiya.

Musabbabin marin Fasto da Portable ya yi

Ya tabbatar da cewa wahayi ya samu da ya mari Faston domin sanin ko na gaskiya ne kuma jabu.

Har ila yau, ya yi tatali da caccakarsa da ake yi wai ya ci zarafin bawan Allah wanda ke wa'azi ga al'umma.

Ya kara da cewa babu wanda zai yi nasarar hallaka shi saboda kowane lokaci Ubangiji yana tare da shi.

Kara karanta wannan

"Ba fashe wa dam ta yi ba:" Gwamnati ta fadi ainihin dalilin ambaliya a Maiduguri

Mawaki Portable ya kwadawa Fasto mari

Kun ji cewa mawakin Najeriya, Habeeb Olalomi Badmus ya mari wani Fasto da ke wa'azi kusa da shagonsa na siyar da kayan shaye-shaye.

Mawakin da ake kira Portable ya gargadi Faston da ya bar kusa da shagonsa inda ya ke zargin yana damun abokan huldarsa da suka zo kasuwanci.

An yada faifan bidiyon a kafofin sadarwa inda mutane da dama suka goyi bayansa yayin da wasu ke cewa abin da ya yi ya kauce hanya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.